An garƙame tsohon Akanta-Janar na Nijeriya, Ahmed Idris kan badaƙalar Naira biliyan 109

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

An bayar da umarni a garƙame tsohon Akanta-Janar na Nijeriya, Ahmed Idris da wasu mutane biyu a gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja, akan ha’inci ko zamba cikin aminci na zunzurutun kuɗaɗe na Naira biliyan 109.

Babbar Kotu dake ƙarƙashin jagorancin Alƙali J.O. Adeyemi-Ajayi ita ce ta bayar da umarnin garƙame waɗannan mutane guda uku a ranar Juma’a da ta gabata lokacin da aka gurfanar da su bisa zargin yin zamba da halasta kuɗaɗen haram da ake tuhumar tsohon ma’ajin tarayyar ta Nijeriya.

Alƙalin ya bayar da umarnin a garƙame su a kurkuku har zuwa lokacin da za a saurari buƙatarsu ta neman beli.

Waɗanda aka gurfanar a gaban shari’a tare da tsohon Akanta-Janar ɗin sune Godfrey Olusegun Akindele da Mohammed Kudu Usman.

Yayin da aka gurfanar da su a gaban kuliya a ranar Juma’a da ta gabata, dukkansu sun yi tababar aikata tuhume-tuhume guda 14 da ake yi masu, waɗanda a cikin su ne ake zargin su da karkata akalar kuɗaɗe Naira biliyan 109 kuɗaɗen jama’a.

Idris dai, da farko lokacin da jami’an hukumar hana ta’annati da yin zagon ƙasa wa kuɗaɗen jama’a (EFCC) suka cafke shi, an zarge shi ne da yin almundahana na zunzurutun kuɗaɗe Naira biliyan 80, amma daga bisani lokacin da jami’an hukumar suka zurfafa bincike, sai aka gano gararumar ta kai ta kimanin Naira biliyan 109.

Mista Godfrey Olusegun da Mohammed Kudu Usman an zarge su ne da haɗa baki wajen karkatarwa da halasta waɗannan kuɗaɗe yayin da Malam Ahmed Idris yake riƙe da kujera ko ofishin babban ma’ajin tarayyar ƙasar nan.