An tattauna tsakanin Shugaba Xi na Sin da Biden na Amurka

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Joe Biden, inda suka tabo batutuwan da suka shafi dangantakarsu, da ma sauran batutuwan da suke da moriya iri guda.

Tattaunawar ta gudana ne jiya Alhamis bisa roƙon shugaban Amurka, Joe Biden.

Yayin tattaunawar, shugaba Xi Jinping ya ce duniya a yanzu na fuskantar matsaloli da sauye-sauye da giɓi wajen samun ci gaba da rashin tsaro dake karuwa.

Ya ƙara da cewa, yayin da ake fuskantar sauye-sauye da tashin hankali, ƙasa da ƙasa da alummominsu a faɗin duniya, na sa ran Sin da Amurka za su ja gaba wajen ɗaukaka zaman lafiya da tsaro da inganta samar da ci gaba da kwanciyar hankali a duniya.

Har ila yau, ya ce ɓangarorin biyu na buƙatar hada hannu wajen rage rikice-rikice a yankunan da taimakawa wajen kawo ƙarshen annobar COVID-19 nan ba da jimawa ba, da rage haɗarin hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da taɓarɓarewar tattalin arziki da kare tsari da dokokin kasa da ƙasa ƙarƙashin jagorancin MƊD.

Bugu da kari, shugaba Xi ya ce matsayin ƙasarsa kan batun Taiwan bai sauya ba, kana tabbatar da kare cikakken ’yanci da yankunan ƙasar Sin, muradi ne mai ƙarfi na alummar Sinawa sama da biliyan 1.4.

A nasa ɓangaren, shugaba Joe Biden ya ce duniya na kan wata muhimmiyar gaba, kuma haɗin gwiwar Sin da Amurka ba alummomin ƙasashen biyu kaɗai zai amfanawa ba, har ma da jamaar dukkan ƙasashen duniya.

Ya ce Amurka na fatan barin ƙofar tuntubar juna tsakaninta da Sin a buɗe, domin inganta fahimtar juna da kauce wa rashin fahimta da hada hannu a ɓangarorin da suke da moriya ta bai ɗaya da kuma tafiyar da bambancin dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Ya kuma nanata cewa, manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya ba ta sauya ba a wajen Amurka, kuma ba za ta sauya ba, kana Amurka ba ta goyi bayan ’yancin kan yankin Taiwan.

Mai Fassarawa: Faiza Mustapha