Shin wane ne ya ɗanawa ƙasashen Afrika “tarkon bashi”?

Daga Fa’iza Mustapha

Jaridar The Guardian ta Birtaniya, ya fitar da wani rahoto a baya-bayan nan, da ya yi kira ga cibiyoyin bayar da bashi na yammacin duniya, su sauƙaƙa tsarin biyan basussukan da suke bin ƙasashe masu karancin kuɗin shiga, musamman ƙasashen Afrika.

Wannan rahoton na zuwa ne bayan cibiyar Debt Justice ta Birtaniyar, mai bibiyar yadda ake bayar da bashi tsakanin ƙasashen duniya, ta bankado wasu alƙaluma dake nuna cewa, basussukan da cibiyoyin kuɗi na yammacin duniya ke bin ƙasashen Afrika, ya rubanya wanda ƙasar Sin ke binsu har sau 3, haka kuma kuɗin ruwansu ya ninka na Sin sau biyu.

Tambayar a nan ita ce, shin wane ne ya ɗana wa ƙasashen Afrika Tarkon Bashi?

Batun “Tarkon Bashi” wani abu ne da ƙasashen yamma suka ƙirƙiro, bisa zargi mara tushe da suke wa ƙasar Sin da kakabawa ƙasashen Afrika bashi fiye da kima.

Sai dai, sun tsallake tarin basussuka da kuɗin ruwa da cibiyoyin kuɗi na ƙasashensu suka laftawa ƙasashen na Afrika.

Ƙarya fure take ba ta ’ya’ya. Yanzu ga gaskiya ta fito, amma ƙasashen masu neman haifar da kiyayya tsakanin Sin da aminanta na Afrika, kawai saboda kishin karɓuwar da ta samu, sun yi gum.

Duk wanda ya je ƙasashen na Afrika, zai ga yadda ƙasar Sin ta taimaka wajen gaggauta samar da kayayyaki na ci gaban da kyautatuwar rayuwa, daga kayayyakin more rayuwa, zuwa zuba jari da samar da aikin yi da tallafin karatu da na lafiya da bunƙasa cinikayya da kafa kamfanoni, har ma da dakarun wanzar da zaman lafiya da sauransu.

Haƙiƙa in ma bashi ne, an gani a aikace, domin duk wani katafaren aikin ci gaba a ƙasashen, za a ga cewa mafiya yawansu, Sin ce ta aiwatar. Duk da dimbin bashi da ƙasashen yamma suke bin ƙasashen, ba a ga wani abun a zo a gani da suka taɓuka ba.

Bayan ɓarkewar annobar COVID-19, ƙasar Sin ta amsa kiran ƙungiyar G20 na sauƙaƙa lokacin biyan bashi ga ƙasashe masu karancin kudin shiga, inda kawo yanzu ta sassauta biyan sama da dala biliyan 1.3, wanda ya ɗauki kaso 30 na jimilar shirin. Wannan ya sa ƙasar Sin ta zama kan gaba wajen aiwatar da shirin.

A don haka ne ma, cibiyar Debt Justice ta yi kira ga ƙasashen yamma su tilastawa cibiyoyinsu na kuɗi aiwatar da shirin kamar dai yadda Sin ta yi.

Ina laifin mai taimakawa da kasancewa da kai a kowanne yanayi? Ƙasar Sin ta kasance mai amsa kiran ƙasashen Afrika a ko da yaushe, mai nuna kulawa a gare su, mai kare muradunsu a dandalin ƙasa da ƙasa, mai kai musu ɗauki cikin gaggawa, haka kuma mai jansu a jiki da yayata gogewarta gare su.

Waɗannan kaɗan ne daga cikin dalilan da ya sa ƙasashen ke ƙara aminta da ita. Kamar yadda shugaban Nijeriya ya taba furtawa da aka masa tambaya game da bashin ƙasar Sin, kofarsa a bude take ga duk wanda ke son taimakawa ƙasarsa, kuma ƙasar Sin ta kasancewa mai taimaka mata cikin sauƙi ba tare da sharadi ko katsalandan ba. Kuma shakka babu, irin hakan ne ke kasancewa a wajen dukkan ƙasashen nahiyar.