An rattaɓa hannu kan yarjejeniyar cinikayya da raya tattalin arziki ta Dalar Amurka miliyan 170 tsakanin Sin da ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA

A jiya Alhamis ne aka sanya hannu kan takardun haɗin gwiwa, da ayyukan raya tattalin arziki da cinikayya 14, tsakanin Sin da wasu ƙasashen Afirka da dama, waɗanda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 170.

An sanya hannu kan wadannan takardu ne a jiya Alhamis, yayin taron bunƙasa tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka, wanda ya gudana a birnin Changsha na lardin Hunan dake tsakiyar ƙasar Sin.

Yarjejeniyoyin dai sun ƙunshi ɓangarorin haɗin gwiwar yankuna, da muhimman tsare-tsaren ayyuka, da samar da kuɗaɗen gudanarwa, da fannin hadin gwiwar zuba jari da cinikayya.

Kazalika, a yayin taron, sassan dake lura da cinikayya na lardunan ƙasar Sin 6, su ma sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi na bunƙasa hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya da wasu ƙasashen Afirka.

Taron dai ya samu halartar jakadu 29 daga ƙasashen Afirka 15, da suka hada da na Aljeriya, da Habasha, da Angola, da Ghana, da Kenya.

Bugu da ƙari, mahalartansa sun yi amfani da dandalin taron, wajen yayata manufar yankin gwaji na zurfafa haɗin gwiwar raya tattalin arziki tsakanin Sin da ƙasashen Afirka da aka kafa.

Mai Fassarawa: Saminu Hassan