Badaƙalar Biliyan N109: Kotu ta bada belin Akanta-Janar, Ahmed Idris

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Abuja mai zamanta a yankin Maitama, ta bada belin dakataccen Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris.

Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a kotu ta bada umarnin a garƙame Akanta-Janar ɗin tare da sauran waɗanda suke kare kansu a gidan yarin Kuje kafin sauraren buƙatar belin da suka shigar.

A ranar 16 ga Mayun 2022 jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) suka damƙe Idris bisa alaƙarsa da wawushe biliyan N80.

Bayan ‘yan kwanaki da kama shi ne sai Ministar Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed, ta dakatar da Idris daga aiki.

Ana zargin Idris da abokan cin mushensa da aikata laifuka 14 da suka haɗa da sata da cin amana na kuɗaɗe da suka kai biliyan N109, 485,572,691.9.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Adeyemi Ajayi, ya bada belin waɗanda ake zargin ne bayan cika duka sharuɗɗan belin da EFCC ta gindaya musu.