Firanministar Birtaniya, Liz Truss ta yi murabus

Daga BASHIR ISAH

Ƙasa da watanni biyu da rantsar da ita, Liz Truss ta yi murabus a matsayin Firanministar Birtaniya.

Ms Truss ta ce ta yi murabus ne saboda gazawarta wajen cimma bukatun al’umma wanda aka zabe ta don ta aiwatar.

A ranar Alhamis Truss ta bayyana murabus din ta ga manema labarai a yankin Downing.

‘Yan majalisar kasar daga jam’iyyarta ta Conservative suka bukace ta da ta yi murabus saboda dalilai na kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Akalla jami’ai biyu daga mukarrabanta su ma sun bi sawunt Truss sun yi murabus.

Ta ce ya zuwa mako mai zuwa za a zabi sabon Firaministan da zai maye gurbinta.