Gara hukumomin soja da na ’yan sanda a Nijeriya – Ladi Audu Baƙo

“Asalin alaƙarmu da namun daji”

Hajiya Ladi Audu Baƙo, matar Gwamnan Jihar Kano na farko, Alhaji Audu Baƙo, ta rasu a ranar Laraba, 5 ga Afrilu, 2023, tana da shekaru 93 a duniya. Allah ya gafarta mata. Ɗiyarta Zainab Audu Baƙo ce ta sanar da rasuwar a Birnin Kano. BLUEPRINT MANHAJA ta ci karo da wata tattaunawa da aka yi da marigayiyar a lokacin da ta ke raye. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
 
Hajiya, yaushe aka haife ki, kuma wacce makaranta kika yi?

Ba lallai ne ku samu dukkan abinda kuke nema ba, saboda ƙwaƙwalwar ta yi rauni da yawa. Amma duk da haka, Sunana Ladi Audu Baƙo, kuma wannan shi ne sunan da na shahara da shi a faxin duniya. An haife ni a Sabon Gari ta Zariya kusan shekaru 95 da suka gabata. A lokacinmu ba sunayen titina, amma zan iya tunawa titinmu a wancan lokaci ana kiran sa da Layin Magajiya. A wancan lokacin mata ba su da alfarmar damar karatu kamar yanzu. Duk da haka a wancan lokacin azuzuwa an tsara su da Mataki na 1, Mataki na 2 da sauransu. Na yi makarantar Mishan a wancan lokaci har na kai ga Mataki na 2, kafin a yi min aure Ina da shekaru 14 da haihuwa.
 
Iyayenki ma ’yan Zariya ne?

Iyayena zuwa suka yi Zariya daga Jihar Tsakiyar Yammaci ta wancan lokacin, suka zauna a Sabon Gari. Wannan shi ne dalilin da ya sa na taso a Zariya.
 
Ya za ki kwatanta rayuwa a zamaninku da kuma yau?

Ai sam ma babu haɗi. Rayuwar da ta fi ta yau nesa ba kusa ba. Komai na da ya fi sauƙi da salama. Ba mu da matslolin da muke da su a yau. Kowa harkar gabansa yake yi.
 
Kin ce kin yi aure tun ki na ‘yar shekaru 14. Ko Marigayi Audu Bako shi ne mijinki na fari?

A’a, Marigayi Audu Bako, Allah ya ji ƙan rai, ba shi ne mijina na fari ba. Mijina na fari wani ne daban.

Shi ma tsohon mijin naki haifaffen Zariyan ne?

A’a, shi ma zuwa ya yi. Ya zo Zariya daga wani ƙauye da ake kira Rahama a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Soba ta yanzu. Ya zauna a Sabon Garin Zariya, kamar dai iyayena. Ɗan kasuwa ne mai yin safarar citta. Sarkin Zazzau na wancan lokacin shi ya aurar da ni ga mijina na farko.

Ki na nufin sarki mai ci a yanzu?

A’a, sarkin yanzu ai yaro ne a wajena. Sarki Aminu shi ne waliyyina. Na taso a gidansa. Kuma har yau mu na da kyakkyawar aIaƙa da iyalinsa.

Ta yaya kuka haɗu da Marigayi Audu Baƙo?

Mun haɗu da shi a Sabon Garin Zariya. Ba ni ce matarsa ta fari ba. Haɗuwata da shi ta kasance abin mamaki. Na haɗu da shi a lokacin da yana jami’in ɗan sanda a garin Zariya. An yi masa canji zuwa Zariya ba da daɗewa ba. A lokacin Ina da lawaye; Gambo Sawaba da kuma Marigayiya Hajiya Kaka Tudun Wada, kuma gurin haɗuwarmu ta ƙawaye ya kasance gidan su Gambo Sawaba ne.

A lokacin, mu da ba mu da mazaje samarinsu kan zo su ba mu kuɗi mu sayi kai da ƙafar kaji. Ranar da muka haɗu da Audu Baƙo, yayar Gambo Sawaba ce ta sa ni wanki. Da na zo zan tsallaka titi, sai  ga Audu Baɗo yana tuƙa kekensa. Sai ƙanwata da muke tare ta ga ya ƙura min ido. Sai ta ce masa ɗan uwa ka daina yi mata kallon ƙurilla, ba ba ka ita zan yi ba. Bayan wannan haɗuwar, sai ya yi ta bi na. Kullum ya zo sallama da ni, sai a ce ga ɗan sanda nan ya zo neman ki. Sai na ce, wai me zan yi da ɗan sanda?

A lokacin ba mu saba da ’yan sanda ba a Zariya, mun fi sabawa da sojoji. Gambo Sawaba ita ke takura min na fita wajensa, wai kada na wulaƙanta shi. Sai ya yi min kyautar Sulai Biyar. A wancan lokacin sai na zama mafi arziki a tsakanin tsarorina. Duk da haka muka qi yarda mu nuna masa gidanmu na asali. Sai ran nan tsautsayi na zo fitowa daga gidanmu, muka haɗu da shi.

Daga nan ya san gidanmu kuma ya fara kawo min ziyara can koyaushe. Abu kamar wasa sai na afka matsananciyar soyayyarsa. Har ta kai zan iya komai saboda shi. Kuma soyayyar tana nan har yau. Wannan ya sa Sarkin Zazzau Aminu ya amince da aurenmu da shi.
 
Za ki iya tuna shekarar da kuka yi aure da shi?

Wallahi ba zan iya tunawa ba. Amma dai na san ni Ina da shekaru 19 shi kuma yana 25 sanda muka yi aure.

Ya aka yi kuka dawo Kano?

Ka san yanayin aikin ɗan sanda. Mun zaga jihohi da dama a faɗin tarayyar ƙasar nan inda ake cilla mu. Kuma zuwanmu Kano ma yanayin canjin wajen aikin da aka saba yi mana ne.

Za ki iya tuna yadda marigayin maigidanki ya zama gwamnan Kano?

Eh, yana gonarsa ne a Kaduna a wancan lokacin sanda ya samu saƙo yana umartar sa cewa ya gaggauta dawowa Kano a cikin kwana biyu. Ina zaune a gidanmu na kan titin.

Swimming Pool Road a Kaduna, ya shigo ya ce na haɗa kayana za mu koma Kano. A ranar muka tafi muka bar kayanmu. Su kuma kayan namu suka biyo mu bayan sati biyu da tafiyarmu. A wancan lokacin ba wanda zai ba ka sanarwa kafin a yi maka canjin aiki. Kuma da an kira, da ka tafi. Akwai garin da aka tura mu, kafin ma mu ajiye kayanmu an sake yi mana canjin gari. Haka muka sake wucewa.

Ya ki ka ji lokacin da ana ta sukan marigayin mijinki a lokacin da yana kan kujerar gwamna?

To, a lokacin kawai ƙarfafa masa gwiwa na dinga yi, saboda na san suka yana daga cikin ƙalubalen rayuwar ɗan adam. Kuma kada ku manta da irin son da na ce muku yana yi min. Shi ya sa duk sanda aka soke shi a wajen aiki, sai na ga ya kamata ni kuma na tsaya masa. Na kan ce masa ya sa a ransa mutane ba za su yaba da aikinsa ba a yanzu sai sanda ba ya nan, kuma hakan ya qara masa ƙwarin gwiwa sosai.  Kuma sai ga shi hakan ta tabbata duba da yadda a yanzu mutane suke yaba wa Audu Baƙo.
 
An san ku da ɗabi’ar ajiye namun daji a gidanku. Me ya ke nishaɗantar da ke, kuma ina ku ka kai dabbobin?

Gaskiya ne. Amma wannan ya samo tarihi ne. Akwai wata rana da wasu mutanen wani ƙauye suka tsinci jariran zakuna biyu da ambaliya ta ciyo ta kawo gonakinsu, suka kawo min. Sai na karve su hannu bib-biyu na cigaba da kiwata su, kuma zakunan mace ce da namiji. Saboda ranar Juma’a aka kawo min su, sai na sa musu Ɗanjuma da Jummai. Amma daga baya sai Jummai ta mutu. Shi Ɗanjuma mun shaƙu da shi sosai har kwanciya yake tsakaninmu da ɗiyata Zainab. Har magana nake masa ma ya ji. Amma matsala ɗaya, su zakuna suna da riƙo da son ramuwa. Akwai sanda ya kai hari ga wani yaron gidana. Allah ya sa na zo, kafin ya aikata ɓarna gare shi na tsawatar.

Bayan faruwar lamarin, Audu Baƙo ya gargaɗe ni cewa, na yi hankali kada Ɗanjuma ya jawo min matsala. Da ma shi can ba shi da ra’ayin ajiye namun daji. Burinsa ya kasance a gona kullum. Daga nan sai ya gina gidan Zoo ɗin nan na Kano. Ya ba da kyautar Ɗanjuma a matsayin dabbar farko a gidan Zoo ɗin.

Ko har yanzu Ɗanjuma yana raye?

Ba na tsammanin hakan. Ina jin ya mutu. Ina son namun daji. Bayan nan ma na cigaba da kiwata dabbobin daji.

Ya ki ka ji lokacin da Janar Murtala ya sauke mijinki daga muƙaminsa?

Ina nan Kano a lokacin. Kuma babu wani abin tashin hankali, don ba a illata mu ba. Kuma mijina da ma ya riga ya yi ƙarfi sosai a harkar nomansa. Yarana dukkansu sun shiga makarantu. Wannan gidan da nake ciki an saya min shi ta hanyar karo-karo da kwamishinonin Jihar Kano suka yi.
 
Hakan na nufin mijinki bai bar kadarori ba kenan?

Ba zan iya cewa bai bar komai ba. Amma abinda na sani shi ne, ya biya basussukan da ake bin sa kafin ya mutu. Irinsu ne shugabannin wancan lokacin, kamar yadda na gaya maka hatta gidan da za mu zauna bayan rasuwarsa sai da aka saya mana ta hanyar karo-karo.

Bayan rasuwar mijinki, kin fara yin wasu abubuwa ne don ɗaukar ɗawainiyar kanki?

Ni ban fara kowacce sana’a ba. Tun da jajayen sawayena da ma ni cikakkiyar matar aure mai zaman gida ce. Don haka kawai, sai na cigaba da kula da yarana.

Kin ce ba kya sana’a, amma waye yake kula da ɗawainiyarki?

Ban san me ya sa mutane suka damu da wannan ba. Ba na son cin fuskar kowa, amma shugabannin wannan zamani da zarar sun sa kuɗi sun sayi kujerar mulki, ko waiwaye ba sa yi. Ba kamar zamaninmu ba. Daga hukumar ’yan sanda har gwamnatocin Kano da suka shuɗe ba wanda ya ba mu komai. Misali dai, Kabiru Gaya lokacin yana gwamna ya ɗauki nauyin ɗana, don nema masa magani a ƙasar waje. Ina tsammanin sauran gwamnatocin ma suna taimakawa, amma yanzu abin ya zama tarihi.

Amma a ɓangaren hukumar ’yan sanda, ba na so na zagi kowa, amma ni ban tava ganin hukuma irin ta ’yan sanda ba. Lokacin da kake aiki da su ne kawai kake mutum. Da zarar ka tafi, shikenan. A ganina ma gara hukumar soji sosai a kan ta ’yan sanda.

Ki na nufin ba wani abu da ki ke samu daga gwamnatin Jihar Kano a matsayinki na iyalin tsohon Gwamnan Kano?

Ba abinda muke samu. Iyalin Audu Baƙo ba sa samun komai daga gwamnati. Yanzu abinda na shagaltu da shi shi ne, addu’ar Allah ya ji qan sa. Mun yi zaman lafiya bisa doron so da ƙauna. A zamaninmu ne ake samun soyayyar gaskiya. Shi ya sa na kasa manta marigayin mijina. Yanzu ba komai sai soyayyar ƙarya.

Hajiya, har yanzu ki na da yara?

Eh, har yanzu Ina da yara maza guda uku da yara mata ma uku. Amma guda daga ciki ya rasu. Yanzu Ina da yara mata uku, maza biyu. Amma mijina yana da wasu yaran. Da ma na gaya muku ba ni ce matarsa ta fari ba.

Hajiya Ladi Baƙo ta rasu ne a ranar 5 ga Afrilu, 2023. Allah ya ji ƙan ta, ya sa ta huta. Ya yafe mata kurakurenta.