Ghana ta ci tarar wani kamfani Dala miliyan shida don silar mutuwar mutane 13

Gwamnatin Ghana ta ci tarar wani kamfanin haƙar ma’adinai tarar Dala miliyan shida, saboda haɗarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 a watan Janairu sakamakon fashewar motar da ke ɗauke da nakiya.

Fashewar nakiyar ta haifar da ƙaton rami da kuma rushewar gidaje da dama kusa da birnin Bogoso da ke da nisan kilomita 300 daga birnin Accra.

Hukumar agajin gaggawa a ƙasar ta ce, bayan mutuwar mutane 13, haɗarin ya raba mutane sama da 700 da muhallinsu.

Ministan ma’adinai Samuel Jinapor, ya sanar da cewar, kamfanin Maxam Ghana da ke sarrafa nakiyoyin, ya saɓa wa dokokin hakar ma’adinai wajen safarar nakiyoyin.

Jinapor ya ce, sakamakon nazarin da suka gudanar akan haɗarin, ya sanya tarar Dala miliyan guda akan kamfanin Maxam.

Ministan ya ce, bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin kamfanin, Maxam ya amince ya biya wasu ƙarin Dala miliyan 5. Tuni aka rufe kamfanin domin gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *