Kwamishinan Zamfara ya ɗauki nauyin auren ’yan mata marayu 20

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kwamishinan ma’aikatar raya otal-otal da yawon buɗe ido na jihar Zamfara Hon. Abubakar Abdullahi ya ɗauki nauyin auren yara mata marayu su 20 a ƙaramar hukumarsa Tsafe.

Da yake jawabi yayin bikin ɗaurin auren da aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin Tsafe ranar Lahadin da ta gabata, mai martaba Sarkin Tsafe Alhaji Muhammad Bawa ya yaba wa kwamishinan bisa jajircewarsa na inganta tarbiyya da rayuwar marasa galihu a yankin.

Sarkin ya yi kira ga masu arzikin yankin da su yi koyi da shi wajen inganta rayuwar marasa galihu a masarautarsa.

“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga masu hannu da shuni a masarautata da su yi kwafin Hon. Abubakar Abdullahi Tsafe kan yadda za a inganta rayuwar marasa galihu a yankin.”

A nasa jawabin, Gwamna Bello Mohammed Matawalle wanda kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Hon. Nasiru Mu’azu Magarya ya wakilta, Hon. Abubakar Abdullahi bisa ga gaggarumar gudunmawar da yake bai wa bil’adama a karamar hukumar sa.

Matawalle ya bayyana cewa ƙoƙarin ɗaukar nauyin ‘yan mata da maza 20 da kwamishinan otal da yawon buɗe ido na jihar, Hon.

Abubakar Abdullahi Tsafe ɗaurin auren yana maraba da ci gaba, inda ya ƙara da cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen inganta tarbiyyar al’ummar yankin.

A jawabin maraba, Hon. Abubakar Abdullahi Tsafe, ya bayyana cewa za a ci gaba da irin wannan karamcin ga masu ƙaramin ƙarfi a yankin ƙaramar hukumar sa ta Tsafe dake jihar ta Zamfara.

Ya ƙara da cewar, kowace amarya ta samu kayan ɗaki, buhun shinkafa, buhun madara, yayin da aka biya wa angwaye sadakin kowace yarinya.

“Za mu ci gaba da gudanar da sadaukar da kan mu wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar al’ummar mu, musamman marasa ƙarfi a ko yaushe don rayuwar su ta inganta,” Abubakar Abdullahi Tsafe ya ce.

Ya yi kira ga ma’aurantan da su mutunta zamantakewar su saboda tsakanin su da Allah tare da kare tabbatar da sun zauna lafiya da juna don samun zuri’a ingantatta.