Gidauniyar Jema’a ta rantsar da sabbin shuwagabanni

Daga ABUBAKAR LABARAN a Kafanchan

Gidauniyar Jema’a wadda ke da hedikwata a Kafanchan cikin Ƙaramar Hukumar Jema’a a Jihar Kaduna, ta rantsar da sabbin shuwagabannin ta da su ja ragamar gidauniyar tsawon shekara uku.

An gudanar da gagarumin taron rantsar da sabbin shuwagabannin ne cikin makon nan a babbar sakandaren Isah Mohammed da ke Kafanchan, inda shugaban kwamitin zaɓen, Alhaji Adamu Makadi ya bayyana cewa rantsuwar ta biyo bayan zaɓen da aka yi ta hanyar yarjejeniyar sulhu da dukkan zaɓaɓɓu ba tare da yin zaɓe ba.

A nasa jawabin dangane da taron, shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Bala Adamu ya ce an zaƙulo shuwagabannin ne daga sassa uku da suka haɗa da: Kafanchan, Kaduna da kuma Abuja.

Da ya samu wakilcin Alhaji Abdulrazak Ramat Muhammad, sakataren kwamitin, ya ce mambobin su da suke biyan kuɗin ƙungiya a kodayaushe su ne kawai suka cancanta a zaɓen.

A nasa jawabin, shugaban gidauniyar mai barin gado, Alhaji Abdullahi Zubairu ya taya sabbin shuwagabannin murna, kana ya hore su da su kasance masu ƙwazo akan ayyukan su wajen kawo zaman lafiya da haɗin kai, girmamawa da fahimtar juna a tsakanin mambobi da makwaftan, don kawo ya yankin cigaba mai ma’ana.

Alhaji Zubairu ya ce ya gamsu a matsayin sa na shugaban gidauniyar tsawon shekara takwas, inda ya samar da ɗumbin nasarorin da suka haɗa da samar wa al’ummar yankin da asibiti, wadda mutane da wasu ƙungiyoyi da cibiyoyi suka bada haɗin kai da goyon baya wajen samar da ita. 

Ya hori sabbin shugabannin da su kasance masu koyi da tsoffin shuwagannin wajen saka kishi da son cigaban al’ummar Jema’a, ya roƙe su da su zama kodayaushe ƙofar su a buɗe take wajen tuntuɓar Sarkin Jema’a, Alhaji Muhammad Isah Muhammadu da wasu mambobin gidauniyar kafin zartar da kowane irin hukunci.

Da yake jawabin godiya, sabon shugaban gidauniyar, Alhaji Abdullahi Hassan Mohammed ya bayyana godiyarsa ga Allah da kuma al’ummar Jema’a akan nauyin da suka ɗora musu na shugabantar su, sannan ya jinjina wa kwamitin gudanar da zaɓe wanda Alhaji Adamu Makadi ya jagoranta wajen gudanar da zaɓen cikin nasara.

Alhaji Abdullahi ya yi alƙawarin za su ɗora daga inda tsoffin shuwagabanni suka tsaya, ta hanyar samar da ababen more rayuwa wa jama’a.

Ya kuma roƙi dukkan masu hali da su cigaba da taimaka wa gidauniyar, don cigaba da gudanar da ayyukan ta, sannan ya roƙi waɗanda ba su yi rajista ba su yi ƙoƙarin yi.

Shugabbin da suka sha rantsuwa sun haɗa da Alhaji Abdullahi Hassan Mohammed: Shugaba, Alhaji Bashir Idris: Mataimakin Shugaba 1, Alhaji Rilwanu A, Ladan: Mataimakin Shugaba 2, Alhaji Ashafa Ladan: Sakatare-Janar, Sanusi Gidado Bala: Sakataren Shirye-shirye da Alhaji Haruna Salihu a matsayin Mataimakin Sakataren Shirye-shirye.

Sauran sun haɗa da; Mallam Magaji Mande: Sakataren Kuɗi, Alhaji Ibrahim Bala: Ma’aji, Mallam Hayatu Adamu: Mai Bincike Kuɗi, Alhaji Sanusi Gidado Bala: Jami’in Hulɗa da Jama’a, Hajiya Rahina Tukur: Shugabar da Hajiya Salamatu Sabuwa Aliyu a matsayin Mataimakiyar Shugabar Mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *