Gurɓatar yanayi: Kamfanin Shell ya amince da biyan diyyar Yuro miliyan 15 ga manoman Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Bayan doguwar Shari’a da aka shafe tsahon shekaru ana yi, Kamfanin tace man fetur na ƙasar waje, Shell ya amince da biyan diyyar wuri na gugar wuri har Yuro miliyan 15 ga wasu manoman Kudancin Nijeriya guda 3 da ƙauyukansu a yankin Neja Delta.

Kotun mai zamanta a ƙasar Holan ita ta yanke wannan hukunci tun a shekarar 2021. Inda ta umarci kamfanin da ya biya diyyar garin man fetur da ya faru ta sanadiyyar kamfanin Shell a wasu ƙauyuka a Neja Delta a tsakanin shekarar 2004 da 2007.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun a wancan lokaci manoman tare da taimakon abokan arziki a faɗin Duniya a ƙasar Netherlands, da kuma lauyoyi Nijeriya guda biyu, Chima Williams da Channa Samkalden, suka shigar da ƙara a shekarar 2007 a kotun Duniya da ke Hague, a game da gurbata yanayin da man fetur ya jawo a gonakin ƙauyukan Goi, Oruma da Ikot Ada Udo.

Ƙauyen Goi yana cikin Oruma, ta jihar Bayelsa yayin da Ikot Ada Udo take cikin garin Akwa Ibom dukkan a yankin Neja Delta dake Nijeriya.

A wani jawabi da aka gudanar a ranar Juma’ar makon da ya gabata a Benin tare da masu ruwa da tsaki tare da ‘yan jaridu suka yi taron tattaunawa an bayyana umarnin da kotun ta yi ga kamfanin Shell ya biya diyyar Yuro miliyan 15 da kuma amsar umarnin da kamfanin ya yi cewa zai biya wani mataki ne na nasara ga kowa.

Mista Jakpor ya bayyana cewa, kamfanin kuma ya ce zai gyara tsarinsa da yake gano inda yoyo yake, don kiyaye samun gurbatar yanayi a gaba.

Haka shi ma lauyan kes ɗin Mista Chima Williams, ya bayyana cewa, wannan nasarar ta samu ne sanadiyyar jajircewar manoman da al’ummar ƙauyukan kuma hakan abin koyi ne ga da zai zaburar da mutanen yankin da sauran da ma sauran yankunan a ko’ina suke.

Ya ƙara da cewa, in dai har za a ci nasara a kan kamfani kamar Shell, to ba makawa ba wanda ya isa ya guje wa Shari’a.