‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Kanal Lawal Yandoto a Zamfara

Daga MUHAMMAD SANUSI a Gusau

‘Yan bindiga a Jihar Zamafara su ui garkuwa da Kanal Lawal Rabi’u Yandoto (mai ritaya) a kan hanyarsa daga Gusau zuwa mahaifarsa ‘Yandoto a Karamar Hukumar Tsafe a jihar.

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Blueprint Manhaja ta waya cewar, da yammacin Lahadi ‘yan bindigar suka tare Kanal Yandoto inda suka yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa biyu da wasu mutane biyu.

Majiyarmu ta ce, “Mun ji ƙarar harbin bindiga a kusa da garinmu na Yandoto kuma kowa ya fara gudun tsira don samun mafaka”.

Ya ce nan take bayan sun dakatar da harbe-harben, al’ummar yankin suka fahimci cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da tsohon jami’in sojan a hanyarsa ta komawa gida daga Gusau babban birnin jihar inda suka bar motarsa ​​babu kowa.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *