Ƙungiyar START WANEP ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Kano

Daga BABANGIDA S GORA a KANO

A ranar Litinin da ta gabata ne Gidauniyar Wanzar da Zaman Lafiya da Samar da Dumukuraxiyya mai Ɗorewa (DAG), haxin gwiwa da ƙungiyoyin START da WANEP sun gudanar da taron matsakaitan masu ruwa da tsaki dan magance matsalolin tashe-tashen hankula a Jihar Lano.

Da yake jawabinsa yayin taron na kwana biyu da ya gudana a ɗakin taro na tunawa da Malam Aminu Kano, Shugaban Ƙungiyar ta DAG na ƙasa, Dr. Mustapha Muhammad, ya ce wannan horo na kwana biyu sun haɗa shi ne don wayar ma da waɗanda aka zavo bisa cancanta da duba irin yanayin gudunmuwar da suke badawa a unguwanni da suke zaune a shiyyiyo 3 da ke jihar ta Kano don ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a kan abin da ya shafi tsattsauran ra’ayi.

Dr. ya ce buƙatar wannan taro anan shine wayar wa da mutanen kai yadda ƙungiyoyin da ake fama da su a duniya dan haka a nan Nijeriya ma akwai matsalolin ƙungiyoyin da ake fama dasu kamar Boko Haram, IPOB, masu garkuwa da mutane harkokin daba, kwacen wayoyi da ya kamata mazauna unguwanni sun san hanyoyin da za su magance matsalolin kafin ya girma.

Haka zalika, ya ce, horon na samun tago ma shi ne daga waɗancan ƙungiyoyin na hukumar bincike ta duniya watau START da Yar’uwarta WANEP, inda wannan ƙungiya ta samar da zaman lafiya da domukuraɗiyya ta DAG ke sa ido domin ganin an cimma wannan ƙudurin don rage tashe-tashen hankula da ke ƙara ƙamari a yankunanmu.

Ya kuma ƙara da batun cewa dole ne matsayin su na fararen hula su shigo don taimakawa gwamnati da irin waɗannan shirye-shirye da zasu taimaka wajen samar da zaman lafiya.

A ɓangaren wasu da suka samu halartar bitar da wakilinmu ya tuntuve su yadda suka fahimci wannan horo mai suna kwamured Barda Ibrahim Sulaiman ya ce a wannan zama ya fahimci kyale mutum cikin yanayi halin da yake ciki yana qara taimakawa wajen ƙara shigarsa damuwar da ka iya tunzura shi ya aikata laifin da ya wuce misali.

Ya ƙara da cewa, lallai a wannan bita ya koyi yadda zasu taimaka wajen ganin sun daƙile wasu tarzoma ko tashin hankali a cikin unguwanni da mutane ke zaune don haka ya tabbatar zai ƙara ba su ƙaimi na daƙile matsalolin na tashin hankali.

Ita ma Jummai Lado ta ce, lallai ta samu ƙarin haske akan wannan bita matuƙa ta yadda zasu kawo ɗauki dangane da irin waɗannan matsalolin da ke bijirowa da yawan lokuta a unguwanni da suke zaune.

Daga ƙarshe mahalarta taron sun tabbatar da irin abubuwan da za su yi madamar irin wannan ƙalubale sun taso da waɗanda yakamata su tunkara da irin abubuwan da yakamata a yi don magance irin wannan matsalolin tare da zimmar komawa don sanar da mazauna yankunan su irin abin da suka koya, haka zalika waɗanda suka gabatar da bitar na kwana biyu ga mahalartan sun haɗa da Dr. Mustapha Muhammad DAG, Malam Aliyu, Sadiq Mustapha Muhammad sai Abdulbaqi Muhammad.