ASUP ta yi fatali da umarnin gwamnati kan haramtawa makarantun kimiyya bada digiri

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Ƙasa (ASUP) ta yi watsi da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar ga makarantun na su daina bayar da takarsar shaidar digiri.

Gwamnati ta hannun Hukumar Kula Da Ilimin Fasaha ta Ƙasa (NBTE) a makon da ya gabata ta haramtawa makarantun kimiyyar na ƙasar bayar da takardar digiri.

A cikin gaggawar mayar da martani ga umarnin gwamnati, Shugaban ASUP na ƙasa, Anderson Ezeibe, ya ce, ƙungiyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba da wannan umarni, kuma ya dage cewa makarantun na da ƙarfin da ake buƙata na kayan aiki da kuma manhajoji da ake buƙata don bayar da digiri.

Ezeibe ya yi mamakin dalilin da ya sa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta ba da irin wannan umarnin ga jami’o’in da ke ba da takardar difloma da sauran takardun digiri ba.

A cewarsa, umarnin wani wariya ne ga masanan kimiyyar ƙere-ƙere ta Nijeriy.

Ya yi gargaɗin cewa, “Ƙungiyarmu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba da wannan umarnin. A maimakon haka, za mu ƙara samun izza wajen neman ’yancin kanmu daga makircin ruguza tsarin kimiyyar ƙere-ƙere ta Nijeriya gaba ɗaya ta hanyar irin waɗannan munanan manufofin.”