Yari ya yi kukan murna da ganin dandazon masoya a Anka

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari wanda kuma shi ne shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamna Bello Matawalle a zaɓe mai zuwa ya zubar da hawaye kan ɗimbin magoya bayan Jam’iyyar APC da ya gani ranar Lahadi a garin Anka, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara.

Yari wanda magoya bayan Jamiyyar APC suka buƙaci ya bai wa ɗimbin magoya bayansa kulawarsa domin nuna goyon bayansu gare shi ya sanya shi zubar da hawaye saboda farin ciki.

A jawabinsa, Abdulaziz Yari ya bayyana jin daɗinsa kan irin goyon bayan da magoya bayan APC suka nuna a garin Anka.

Ya ce rashin tsaro da ake fama da shi sakamakon ayyukan ‘yan bindiga matsalar ta fara ne a lokacin shugabancinsa, yana mai jaddada cewa idan aka ba Matawalle damar shugancin jihar karo na biyu, zai ƙara zage damtse wajen ganin an dawo da zaman lafiya a faɗin jihar.

Daga nan ya yi kira ga magoya bayan Jam’iyyar APC da su zaɓi Matawalle don ba shi damar samar da ƙarin ababen more rayuwa a mulkin dimokuraɗiyya ga ‘yan jihar da kuma ƙara haɓaka tattalin arzikin jihar.

Yari wanda yake takarar ɗan Majalisar Dattawa na mazaɓar Zamfara ta Yamma a zaɓe mai zuwa, ya sha alwashin shiga duk lungu da saƙo domin gudanar da yaƙin neman zaɓensa da na Gwamna Matawalle domin samun nasarar APC.

A nasa jawabin, Gwamna Matawalle ya nuna jin daɗinsa da irin goyon bayan da magoya bayan jam’iyyar APC suka nuna a lokacin yaƙin neman zaɓen shi a garin Anka tare da alƙawarin tabbatuwar cigaban jihar idan har ya samu damar wa’adin mulki karo na biyu a zaɓe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *