Me ya sa wasu ’yan sanda ke buɗe wuta kan marasa laifi?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ba ma wani baƙon abu ba ne yadda wasu baragurbi a cikin ’yan sanda ko ma sojoji da sauran jami’an tsaro kan buɗe wuta kan waɗanda ba su yi laifin komai ba kuma bisa dalilin da bai taka kara ya karya ba.

Wannan na jawo ɗar-ɗar a zuciyar fararen hula ga wannan aji na jami’an da a ke biya daga baitul-malin gwamnati su riqa juya makamansu, su na hallaka jama’a ba gaira ba dalili. Haƙiƙa mutane da yawa sun ran su daga albarusan wasu daga jami’an tsaro da ke keta ƙa’idar aiki. Abun da ya kamata ya zama ya na faruwa shi ne da zarar mutum dan ƙasa nagari ya ga jami’in tsaro riƙe da ƙatuwar bindiga hankalin sa kan kwanta ne amma irin wannan fa ya fara gushewa.

Ba ma kuma lalle sai ta hanyar jami’an tsaro da ke aiki ba takatsantsan ba har ma a kan samu kuskure daga sojojin sama da kan sauke boma-bomai har hakan ya shafi farar hula. Tun abun da ya faru a Rann da ke jihar Borno inda jirgin yaqi ya sauke bom kan wani sansanin ’yan gudun hijira da zaton taron ’, ’yan ta’adda ne har kimanin mutum 50 su ka rasa ransu, a ka fara firgita in an ga jirgin yaƙi na shawagi a yankunan fararen hula. Baya-bayan nan an samu labarin irin wannan kuskuren da ya rutsa da ’yan ƙauyen Matumji a jihar Zamfara yayin da jirgin yaƙi ke bin taron wasu ’yan ta’adda.

Duk da rundunar soja ta nuna ta kashe ’yan ta’adda da yawa amma ba ta ce sam ba farar hulan da ya rasa ran sa ba. Mutanen qauyukan da ke fama da ’yan ta’adda na cikin zullumin hari ta sama daga jiragen yaqi ka iya shafar su. Don haka ya na da kyau a riqa tantance bayanan sirri sosai kafin ɗaukar mataki ko kuma idan ’yan ta’adda sun ruga sun shiga cikin mutan ƙauye don samun kariya, to ya zama akwai sojojin ƙasa da ke jiran ko-ta-kwana da za su shiga don gamawa da su maimakon a cigaba da ruwan boma-bomai.

A gani na duk da gaskiya ni ba kwarerre a lamuran tsaro ba ne amma a inda a kan sadaukar da ran jama’a a farmakin murkushe ’yan ta’adda shi ne idan an tabbatar ’yan ta’addan duk sun tattaru a waje ɗaya kuma marar sa laifi ko jama’ar da ke wajen ba su da yawa, kazalika ya zama in an kai harin shikenan an huta ba sake jin duriyar wani mugun iri. To amma in kawai za a ba da labarin an hallaka ’yan ta’adda dama dama alhali a ranar ko ma gobe za ka ji sun ɓulla ta wani waje a daf da inda a ka kai harin ai da sauran rina a kaba.

Ba wanda zai ce jami’an tsaro ba sa sadaukar da kan su a yaƙin ’yan ta’adda sai dai hakan na buƙatar kula ƙwarai da gaske don kar garin gyaran gira a tsokale ido. Wannan duk misali ne kawai kafin shiga ainihin darasin wannan shafi na ALKIBLA a wannan mako.

Rundunar ’yan sanda ta cafke jami’in ta da cikin ganganci ya harbe wata lauya mai suna Bolanle Raheem a yankin Ajah a Lagos. Kakakin rundunar a jihar Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa tuni a ka kama ɗan sandan da abokan tafiyarsa a ka kuma kai su sashen binciken miyagun laifuka da ke Yaba don gudanar da kwakkwaran binciken musabbabin kisan.

Rahoton ya bayyana cewa, wannan shi ne ma karo na biyu a cikin wata ɗaya da ‘yan sanda a yankin ke harbe farar hula ba bisa ƙa’idar shari’a ko doka ba.

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Baba Usman Alkali ya ba da umurnin gudanar da bincike, ya na mai yin tir da abun da dan sandan ya aikata. Kazalika Alkali ya mika ta’aziyya ga dangin lauyar ya na mai alwashin za a tabbatar da adalci a kan wanda ya aikata laifin.

Rundunar ta ce, za ta yi takarar dokokin aikin ta don hana ’yan bindiga daɗi a cikin ma’aikatan ta sake nanata irin wannan mummunar ɗabi’a. Rundunar dai ba ta bayyana sunan ɗan sandan nan take ba sai daga bisani ta ce ASP Drambi Vandi ne da ya yi wannan aika-aika amma cafke shi na nuna zargin sa da saba ƙa’idar aiki. Don haka riƙe bindiga ba lasisin buɗe wuta kan jama’ar gari ne haka siddan ba.

Hakan ya nuna soke rundunar nan ta SARS da ke dirar mikiya da wuce gona da iri bai sauya yadda wasu ’yan sanda ke amfani da makamai wajen cin zarafin jama’a ba. Ba a rabu da Bukar ba ne an haifi Habu kan wannan ƙalubalen. Labaran ɓoye gaskiya da bayyana karya daga binciken da sashen ’yan sanda ke yi ya zama ruwan dare. Idan ’yan sanda na yi wa kan su kirari da abokan kowa za ka musanta abun da su ka ce da irin waɗannan bayanai na ban takaici da kawo juyayi. In za a tuna an tava samun irin wannan kisa a Abuja a shekara ta 2005 inda wasu matasa 6 duk da ma yawon dare su ka tafi wani kulob a layin Gimbiya da ke unguwar AREA 11 su ka rasa ran su sanadiyyar bindige su da a ka yi a lokacin da za su nufi gida.

Labarin da kowa zai iya bincikawa an yi ma sa taken “APO 6” kasancewar matasan su shida ne kuma su na gudanar da kasuwancin sayar da kayan mota ne a kasuwar kayan mota da ke Apo a Abuja. Bayan bindige matasan ciki har da mace ɗaya an bunne su a wani kabari a unguwar Utako inda bayan bincike a ka gano akasin da kafa kwamitin bincike a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Obasanjo. Bincike ya nuna an tuhumi ’yan sanda 5 da laifin bindige matasan da kala mu su laifin ’yan fashi da makami ne.

Daga bisani kotu ta yankewa 2 daga ciki hukuncin kisa inda ta sake uku daga cikin su. Har zuwa rubuta wannan shafi rahotanni na nuna ’yan uwan marigayan ba su gamsu da hukuncin da a ka yanke ba.

Mun sha samun labarai na birkicewar wasu sojoji da kan ɗauki bindiga su yi ta buɗe wuta a kan hatsaniya kan soyayya da wata mata ko dalilan da ba su taka kara sun karya ba na nuna fin karfi da zuguwa da makaman da ke hannun su cewa hakan na zama tamkar su ne hukuma ko sun fi ƙarfin kowa kamar yadda wasusn su kan zayyana farar hula a matsayin TARKACE ko a taƙaice a Turance “Bloody Civilian” don haka farar hula musamman talaka marar galihu ba komai ba ne kuma cin zarafin sa ba wani ma laifi ba ne.

Yo in ba haka ba yaushe za a samu soja ya tsoma farar hula a cikin kwata don wulaƙanci. Wa ya ba shi wannan hurumi a dokokin aikinsa? Kai wa ma ya ba wa soja hurumin zare bel ya yi dukan farar hula don wani tankiya da duk ma ba ta wuce kan wata yarinya ƙarama ba! shirmen ya kai a yi gagarumin garambawul wajen tantance duk wanda za a dauka a wannan aiki na sadaukar da kai da kishin qasa. Hakanan a ƙara yin jarrabawa ta tankade da rairaya in an samu masu irin wannan jahilci a yi mu su hukuncin da har su bar duniya ba za su sake marmarin aikata irin wannan ɗabi’a abar kyama ba.

Zan yabawa shugaban sojojin ƙasa na yanzu Laftanar Janar Faruk Yahaya wanda ya ba da umurnin korar kare ga sojoji biyu da ke da hannu wajen kisan gilla ga Sheikh Gwani Aisami a jihar Yobe da kuma ɗaukar matakan shari’a a kan su. Haƙiƙa labarin mutuwar Shehun malamin daga zangar ragewa soja hanya a motar sa ya kawo matuƙar juyayi da nuna takaicin har za a samu sojan da zai aikata irin wannan cin amanar. Allah ya hukunta ma dubun waɗannan sojojin ya cika ne don akwai wasu ma da ba mamaki sun aikata wasu laifuka da ba a gano su ba.

Ofishin jinqai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya nuna matuqar juyayin rasa ran jami’ar agaji da ke aiki a Damboa jihar Borno a sanadiyyar buɗe wuta daga wani sojan Nijeriya da ya birkice.

Shugaban ofishin Matthias Schmale a sanarwa ya isar da sakwan ta’aziyya ga iyalin marigayiyar kazalika ya yi fatar samun sauƙi ga direban jirgi mai saukar ungulu wanda ya samu rauni daga akasin da a ka samu.

Schmale wanda ya yabawa gwamnatin Nijeriya don matakan da ta ke ɗauka na haɗa kai don dawo da yanayi mai kyau a arewa maso gabar; ya buqaci gudanar da bincike kan wannan hari na sojan da kuma ƙara ɗaukar matakan hana afkuwar irin hakan nan gaba.

In za a tuna sojan wanda kazalika ya kashe abokin aikin sa ɗaya, shi ma ya baƙunci lahira a sanadiyyar bindige shi da a ka yi don kar ya cigaba da zubar da jinin jama’a haka siddan.

Kammalawa;

Ɗaukar matakin ladabtarwa ga duk jami’in tsaron da ya keta haddin farar hulan da bai yi laifin komai ba zai taimaka wajen daƙile masu mummunar manufa a aikin tsaro kuma zai tsabtace rundunonin tsaro daga miyagun irin da kan yi amfani da makaman hukuma wajen yaƙi da jama’ar ƙasa marasa laifi.