Gwamna Dikko ya ƙaddamar da dakarun tsaron al’umma a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da Dakarun Tsaron Al’umma na Jihar Katsina (Katsina Community Watch Corps) gami da muhimman kayan aiki domin dawo da tsaro a faɗin jihar.

Shafin Katsina Post ya rawaito cewa an gudanar da bikin ƙaddamawar ne a babban filin wasa na Muhammadu Dikko da ke cikin birnin Katsina ranar Talata.

Kalika, bayan ƙaddamar da dakarun su 1,500, Gwamnan jihar ya kuma ƙaddamar da motoci masu sulke ƙirar Hilux guda 70 da kuma babura 700 domin yaƙi da ta’addanci a lungu da saƙo na jihar Katsina.

Taron ya samu halartar fitattun mutane da shugabannin al’umma daga kowane ɓangare na ƙasar nan.

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin Arewa maso yammacin Nijeriya da sauransu, na ga cikin manyan baƙin da suka halarci taron.