Karatun ta nutsu daga masu rawar kai

Daga ƊANLADI Z. HARUNA

Lokacin da na ji labarin an cafke yarinyar nan Fiddausi mai ƙunduma ashariya da barazanar ta da bom ga wasu manya ban yi mamaki ba. Na tabbatar da ƙwarewar jami’an tsaron Nijeriya musamman ma DSS kan abin da suka sa kansu. Ƙwarewar jami’an tsaron Nijeriya ta wuce sanin irin mu ‘yan koko-ciko, karan kaɗa miya.

Sai dai kuma wannan balahira ta sa na ƙara yin amanna da wasu abubuwa kamar haka:

Na ɗaya, kamar yadda na faɗa, jami’an tsaron Nijeriya suna da qwarewa da matuƙar iya bincike ga abin da suka ga damar ƙaddamarwa. Na sha yin aiki da wasunsu tare da jinjina wa dabarunsu na bincike da iya gano inda mutum yake. Yanzu haka, rubutun nan da nake yi, kafin ƙiftawa da bismilla suna iya ganin inda nake.

Kai ko ba ni da waya ma suna iya gangano ni. Sai dai abin tambaya shi ne, me ya sa duk ɗumbin ta’addancin da ake yi da sace ɗalibai da kama mutane babu gaira babu dalili amma an gaza kama kowa sai ‘yan rawar tiktok? Amsar ita ce, wallahi ban sani ba!

Na biyu, tarbiyya ta yi ƙaranci kwarai tsakanin iyaye da ‘ya’yayensu. Da a ce akwai tarbiyya, ‘yar ƙanƙanuwar yarinya irin wannan ba za ta fito duniya tana ƙunduma zagi na keta haddi irin wannan ba, ballantana kuma ta ambaci sunan wani ko wata. Ana cikin wannan hayaniyar sai ga shi ta sake ɓulla da wani bidiyon na zage-zagen.

Ta yiwu ma iyayen ne ke zuga ta a lokutan farko saboda neman suna. Babu mamaki hakan. Wata uwa ta tava zuwa wajena da ‘yarta da waya, tana so a koya maga yadda ake yin tiktok da instagram da sauran wurare. Tana so ‘yarta ta yi suna ko na wata ɗaya ne. Na san yaran da ke sana’ar wankau suna sayen datar hawa tiktok domin neman suna. Ashe da gangan ake zagin ‘yan fim.

Na uku, zamanin nan kowa ta kansa yake yi. Kar ka ga wai ka zama SELE a duniyar gizo, ka yi tsammanin duniya za ta tashi idan ka je hannu. Biri a hannun malamai yake guɗa, idan ya faɗa hannun arna magana ta ƙare. Duk abin da mutum yake yi, ya guji shiga hannun mahukunta bisa laifin ta da husuma ko mugun alkaba’i. Bar ganin kuna tare a duniyar gizo. Sabo da kaza ba ya hana a yanka ta.

Na huɗu kuwa, qungiyar da ke kiran kansu Kwankwasiyya, suna da wata irin ɗabi’a ta namu shi ne namu, naku kuma shi ne nasu. Ma’ana, duk wani da yake goyon bayansu, to nagari ne, idan kuma ya nuna a zahiri ba nagarin ba ne, to akasi aka samu. Wanda kuwa ba nasu ba ne ko mai sukar su ne.

To fa gorin asali ya same shi. Ba ruwansu da Boka ne ko Malam, dan tasha ne ko ɗan boko, Bahili ne ko Mai saukin kai. Kowa ya taba su sai ya ji su. Gorin asali ga wanda ba nasu ba ne, wannan abu ne mai sauki. Ba wa nasu kariya wannan wajibi ne. Irin wannan kuwa ba abin da yake jawowa ƙungiya sai haƙa wa kanta ramin da za a binne ta da ranta. Mu je zuwa dai.

Na biyar kuma na karshe shi ne, shugabanni na da matuqar haƙuri da juriya. Shugabanci ko na ko na dillalin ambuta ne, yana buqatar hakuri da juriya da kau da kai. Dubi dai irin manyan asharoyoyin da ‘yar mitsitsiyar yarinya ta fito gaban duniya tana narka wa manyan mutane shugabanni da wasu ma sun yi jika da ita. Da yake nauyin ba nata ba ne ita kaɗai, sai suka ƙyale ta hukuma domin su ladabtar da ita.

Da ace irin mu masu rawar kai, sai mu ma shiga gaban duniyar mu yi ta lulluƙa mata ashariyoyin da wataƙila ko kakanta na bakwai bai san da irinsu ba. Haka nan sai kafin a ankara duniyar gizo ta cika da zage-zage da tsine-tsine. Sai a bar Hisbah da sintirin yin sulhu da wa’azi inda wataƙila ba zai yi tasiri ba.

Don haka nan. Ni dai ba na goyon bayan kowanne mugun shugaba, amma ba zan iya fitowa na yi ta danna masa ashar ba. Shin tsoro ne da ni ko kuwa hankalina ne ya yi yawa? Wassalam.

Ɗanladi Z. Haruna, Manazarci ne kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum musamman na siyasa. Ya rubuto daga jihar Kano.