Ina ma Atiku zai ji shawarata..!

Daga RAHMA ABDULMAJID

Kamar yadda ‘yan ƙasa suka sani, tsohon mataimakin tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar ya narka kuɗi da lokaci wajen neman Jami’ar Chicagon Amurka da ta bayyana sakamakon karatun Shugaban Nijeriya mai ci wato Bola Ahmed Tinubu, Inda a daren Litinin ne Jami’ar ta amsa buƙatar da wasu dogayen takardu wanda a dunƙule suke gaskata cewa Shugaba Tinubu ɗalibinta ne, amma ba huruminta ba ne adana kwafi na shahadar calibai ba balle ma ɗaliban tale-tale ‘yan 70s ba tunda tuni ta ba su abinsu.

A yayin da ‘yan Nijeriya suka rabu biyu wasu na murna da hakan wasu na kokawa ni kuma sai na tsinci kaina a me neman kafar da zan bai wa Alhaji Atiku shawarar da so samu ne a yayin da Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin ware kuɗi har 25000 don tallafa wa iyalai Milyan 15 da ke fama da raɗaɗin tattalin arziki har na tsawon watanni 3, da ko da mutum dubu 15 Alhaji Atiku ya ware ya ke ba su Naira dubu 10-10 a wata maimakon kuɗin da yake rafka wa harkar neman satifiket ɗin nan da lallai ya fi cika ɗan ƙasa mai kishin talakawa.

Kamar kowane ɗan lelen Nijeriya mai hannu da shuni irin Alhaji Atiku, ba sai ya zama Shugaban qasa ne kawai zai iya tallafa wa ‘yan ƙasar ba, hasali ma abinda Waziri ke yi yanzu ihu ne bayan hari, domin sanin kowa ne ba a Kamfe sau biyu a shekara ɗaya a tsarin Nijeriya. Da an ci zave ɗayan biyu ake yi, aiki ko adawa da aiki, amma na rasa wa ya bai wa Wazirin Adamawa Shawarar ci gaba da narka kuɗi don yin kamfe bayan kamfe.

Kuma ma abin takaicin shi ne, kamfe din da Atikun ya fi ni sanin rashin alfanunsa ta dalilai kamar haka:

Idan dai da na gaba ake gane zurfin ruwa, to Atiku ya fi kowa sanin cewa farfagandar neman shaidar karatu ba ta taba cire Shugaban ƙasa daga karagarsa ba.

Tsohon mai gidan Waziri wato Olusegun Obasanjo ya bayar da irin wannan kafar don neman a tsige Shugaba Jonathan inda a wata Intabiyu ya yi ikirarin cewa Shugaba Jonathan na amfani da laqabin Dakta ba tare da ya kammala PhD ba, kawai dai sakaye zancen Jamiyyar PDP ta yi don ta ci zaɓe. Wato Jamiyyar da mai ƙarar Shugaba Tinubu a yanzu wato Alh. Atiku ke wa takara. Wannan bai cire Jonathan daga mulki ba.

Na biyu, Shugaba Buhari wanda ya shafe kusan shekaru biyar ana masa bita da ƙullin rashin shaidar jarabawar WSSCE shi ma haka aka ci aka suɗe har gaskiya ta fito bayan kotu ta fatattako ƙarar.

Haka, ɗan takarar Gwamna na Jahar Kogi karkashin Jamiyyar PDP wanda Atikun ke mara wa baya yanzu haka wato Fine boy, Sanata Dino Milaye ya yi karyar cewa yana da digiri shida yana neman na bakwai. Sai dai tun ba a je ko ina ba kafar yaɗa labarai ta Sahara ta bankaɗo cewa, cikin makarantu bakwai da Dino ke ikirarin ya shawo madarar ilmi daga wajensu ba su ma san da zamansa ba. Waɗannan makarantu su ne, ABU, da Harvard University da kuma London School of Economics and Political Science.

Har ta kai da Dino ya ga gaskiya za ta yi halinta sai ya dinga kurma ihu yana ƙaryar suma, wai shi ɗalibi ne me Athma, kuma idan aka dame ta da batun shaidar karatu tana iya tashi. Wannan Dan takarar Alhaji Atiku kenan a Jahar Kogi yanzu haka, kuma ma shi ne ke masa wawan sarki a duk kamfe dinsa.

Wai ma idan Nijeriya Alhaji Atiku yake wa wannan faɗan a shekarar 1999 wato shekarar da Atiku yake lamba ta biyu a Nijeriya kuma yana karagar ka-fi Shugaban ƙasa a lokacin, wani Dakta Waliu Balogun ya yi ƙarar Asiwaju kan batun Satifiket din nan dai in da yake cewa bai yarda cewa Asiwaju wanda ya yi takarar Gwamnan jahar Lagos ya yi karatu a Jami’ar CSU din ba, amma har mutumin ya yi asarar wannan ƙara Atiku bai taimaka masa ba sai yanzu da yake da buƙata?

Bugu da ƙari, shi kansa Alhaji Atiku da tasa a gindinsa domin bayanai na shakkun yadda aka yi ya samu digiri na biyu ba tare da ya yi digiri na ɗaya ba. Ban da ma cewa Shi satificet ɗinsa ma gwanda babu ne don cike WAEC ɗinsa yake da tarin F9, amma duba da faduwar da yake a zave ne ya sa aka kau da kai kada abin ya yi masa biy-biyu.

Ba manufar wannan rubutun kare Shugaba Tinubu ba, manufar ita ce mu roƙi Waziri ya yi wa Allah, ya yi wa ma’aiki, ya bar ‘yan Najeriya su ci kuɗinsa a yayin da suka fi buƙata maimakon narka wa a ƙasashen jajaye kuma ƙosassu.

Rahama Abdulmajid marubuciya, mataimakiya ta musamman ga Shugaban ƙasa, sannan mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum musamman na siyasa. Ta rubuto daga Abuja.