Arewa ina mafita? Ya kamata mu farka daga barci ‘yan Arewa!

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI

Hasbinallahu Wa Ni’imal Wakil! ‘Yan bindiga sun kwashi mata a Federal University Dutsen-Ma. Mako biyu da suka wuce sun kwashi mata a Federal University Gusau. Wannan wace irin masifa ce take neman mamaye Arewa? Shin haka za mu zauna mu zuba ido don abin ba akanmu yake faruwa ba ko a kan Makusantanmu?

Ina manyan malamanmu na addini? Ba za a ji muryoyinsu ba sai akan saɓanin aƙida ko siyasa?

Shin ina manyan yan siyasar Arewa? Sai lokacin Kamfe za su san da zamanmu kenan?
Ina manyan sarakunanmu na Arewa? Sai lokacin bukukuwan Sallah za a ji muryoyinsu kenan?

Ina Sarkin Musulmi? Sai Watan Azumi da na Sallah za a ji muryarsa kenan? Ina manyan masu kuɗin Arewa?

Ina ‘yan jaridunmu na Arewa? Sai za su yaxa abinda ya shafi tumasanci da zambo za mu ji muryoyinsu kenan?

Ina manyan salamburuti na Arewa?
Ina masu ganin su ne Elit ko salamburuti na Fesbuk masu yawan mabiya? Sai za ku tallata ‘yan siyasa za mu dinga jin muryoyinku kenan? Ina manyan marubutan Arewa na Littattafai da jaridu da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum?

Ina manyan ‘yan kasuwarmu na Arewa? Ina talakawa mutanen gari? sai zaku zagi ‘yan siyasa za mu ji muryoyinku kenan? Wannan abin fa da yake faruwa a Arewa kar mu ɗauke shi da wasa.

Don Allah mu fito mu yi magana da murya ɗaya. Idan har za mu yi ta magana a kan Maryam Shetty har a ce surutunmu a soshiyal midiya shi ne ya yi tasirin da aka cire sunanta a cikin ministoci, to ya kamata yanzu ma mu haxa kai ko a Soshiyal Midiya ne tunda lalacinmu ya kai duk inda ake zato. Mu yi magana da murya ɗaya har ya Isa inda zai isa don magance mana waɗannan matsalolin na satar mutabe da ‘uan bindiga a Arewa.

Abin ya yi yawa, kuma yana ba ni tsoro. Tabbas idan muka cigaba da yin shiru, zai cimma kowanne sassa na Arewa.

Ina rubutun nan ina kuka saboda takaicin ni Abdullahi Jibril Larabi idan da ‘yar uwata aka sata ya zan ji? Idan da ɗiyata aka sata ya zan ji? Idan da matan da na sani aka sata ya zan ji?

Don Allah ‘yan Arewa mu farka daga nannauyan barcin nan da muke yi.

Abdullahi Jibril Larabi (UNCLE LARABI), marubuci ne kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.