An damƙe mutum biyu bisa zargin kashe ɗan jarida, Hamisu Danjibga a Zamfara

‘Yan sanda a Jihar Zamfara sun damƙe wasu mutum biyu da ake zargi da kashe ɗan jarida Hamisu Danjibga a jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mohammed Dalijan, ya ce ana zargin wani ɗan ɗan’uwan marigayin, Mansur Haruna tare da abokinsa Ibrahim Nababa su ne suka kashe ɗan jaridar.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da aka baje waɗanda ake zargin a Hedikwatar ‘Yan Sanda da ke Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan da jami’ansu suka sunkuya bincike biyo bayan kashe marigayin.

A cewar Kwamishinan, “Babban wanda ake zargi shi ne ɗan ɗan’uwan Danjibga wanda yake zaune tare da marigayin a nan Gusau.

“Ya yi sha’awar shiga aikin soja amma Alhaji Danjibga ya ce a’a: ‘A’a, saboda alamun aikata manyan laifuka da nake gani a tattare da kai, ba zan taɓa zama mai lamuni gare ka don shiga aikin soja ba’.

“Alhaji Danjibga ya kore shi daga gidansa inda ya koma zama da abokinsa Ibrahim Nababa. A nan wajen abokin nasa suka shirya yadda za su yi garkuwa da Danjibga.

“Bayan da suka kammala tsare-tsarensu, sai suka tafi gidansa suka same shi, sun yi ƙoƙarin ficewa da shi daga gidan amma ya turje.

“Ya ce (wato marigayin): ‘Yanzu ɗana kai ne kake so ka aikata mini irin wannan abu. Babu inda zan tafi’. A wannan lokaci ne yaron ya zaro wuƙa ya daɓa masa a ƙirji sau uku.

“Yayin da shi kuma abokin nasa ys sare shi da adda a kai sau biyu. Nan take ya faɗi kuma rai ya yi halinsa. Daga nan suka ɗauki gawarsa suka jefa a sokawe a wata makarantar Islamiyya,” in Kwamishinan.