Ambaliya ta kashe mutum 45 a jihohi 13 – NEMA

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta kashe mutum 45 sannan ta raba wasu 171,545 da muhallansu a jihohi 13.

Ta ƙara da cewa, an fuskancin ambaliyar ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfin da ake samu a wannan damina.

Wani jami’in hukumar mai suna Dapo Akingbade, shi ne ya bayyana hakan a wajen wani taro da aka shirya a Abuja kwanan nan.

A cewar Akingbade, ya zuwa 7 ga watan Oktoba bayanai sun nuna an samu ambaliyar ruwa a jihohi 13, tare da lalata sashen gidaje 22,666, kana gidaje 5,358 sun lalace baki ɗaya.

Ya ci gaba da cewa, ambaliyar ta shafi gonaki sama da 8,754 a tsakanin jihohin da lamarin ya shafa.

Ya ce tuni hukumar ta soma tattara bayanan ɓarnar da ambaliyar ta yi a jihar Adamawa.

“A Adamawa mabaliyar ta shafi mutane da daman gaske. A wajen taron EOC mun ba da shawarar kowace jiha ta samar da tsarin kawo agaji dangane da ambaliya,” in ji shi.