Ƙabilar Kibishi: Masu banƙare wa budurwa leɓe da sunan ado

Masu iya magana na cewa “Allah ɗaya, gari bamban”. Su dai waɗannan bayin Allah suna rayuwa ne a yammacin kogin ‘Omo’ da ke kudu-maso-yammacin Habasha, ana kiransu da ‘Kibishi’.

Bincike ya nuna cewa su dai waɗannan mutane makiyayane, sannan a kan gane yawan dukiyar kowane gida ta hanyar la’akari da yawan dabbobin da suka mallaka.

Addini:

Waɗannan mutane suna da abin bauta wanda suke yi masa laƙabi da ‘Tuma’. Sun yi imani cewar shi dai wannan Tuma ya kasancene a cikin sararin samaniya, bugu da ƙari mutanen sun yi imani da al’matsutsai da kuma ifiritai, sun kuma yi imani da cewar su ɗin a karan kansu na iya sanya ruwan sama ya sauka a lokacin da suke buƙata.

Al’ada:

Inda ranka kasha kallo! Wani abin ban al’ajabi da waɗannan al’umamma shi ne ɗabi’arsu ta fafake leɓen baki, sannan a sanya masa faifayin katako, yanda suke yi kuwa shi ne duk inda yarinya mace ta kai munzalin shekara ‘goma sha biyar’ zuwa ‘goma sha shida’ za a yanka leven bakinta na ƙasa sannan a fafake shi sosai ta yadda zai zamto ya rabu da ainihin mahaɗinsa da haɓarta.

Ba kowa nauyin yin haka ya rataya a wuyanta ba sai mahaifiyarta, bayan an fafe bakin sai a sami ɗan madaidaicin faifayi na katako a sanya mata a leɓen yayin da zai tokare leɓen. Haka za a bar shi har sai lokacin da aka tabbatar wannan ciwo da ke wajen ya warke tas, daga bisani sai a cire wannan a sake sanya wanda ya fi wanda aka cire ɗin girma. Haka dai za a yi ta canja su bisa yanayin girmansu, ma’ana idan aka cire wani sai a sami wanda ya fi shi girma a saka. Za a yi ta canjawa har na tsawon waɗansu watanni, sannan daga ƙarshe sai a saka kanda ake ganin iya bakin girmansa ake buƙata ya kasance a wajen.

A yanzu dai wannan ɗabi’a ta danganta da ra’ayin ita yarinyar da za a yi wa, ma’ana idan tan aso za a yi mata idan kuwa ba ta so, to falillahil hamdu sai a barta ba lallai ba tilas, sai dai har yanzu al’ummar sun yi imani cewar wannan huda na baki alama ce da ke nuni da cewar yarinya ta kai munzali sannan kuma yakan ƙara mata wani daraja da ɗaukaka ta musamman a idon samari.

A cikin al’adunsu akwai horas da matasa ta hanyar koya musu faɗa, har su zamto gawurtattun jarumai, wannan ya samo asali ne sakamakon yawan tashe-tashen hankula da ke wanzuwa tsakanin su makiyaya da kuma makotansu mutanen ‘Nyangatom’ a kan filaye da kuma gonaki.

Auratayya:

Su dai waɗannan mutane sukan gwada jarumtar saurayi da ke neman aure ta hanyar shirya gasa ta musamman wanda da shi a ke tantance samarin ta hanyar duba jaruntakar kowa a gasa. Gumurzun faɗa a ake yi kashirbin a tsakanin maneman auren budurwar, inda taron yakan sami halartar gangamin samari da ‘yan’mata domin su shaida abin da zai wakana. Akan shirya yin wannan gasa a lokacin da aka yi ruwa ya ɗauke, matasan daga qauyukan ‘Suri’ za su halarci taron, ana fara fadan da mutum ashirin zuwa talatin daga kowanne ɓangare sannan a fara karawa na gaba ɗaya. A wannan lokacin za a wakilta masu alhakin kula da wannan gasa, wato alƙalan gasar domin lura da yadda gasar ke gudana.

Ba a nan gizo ke sakar ba, domin kuwa wannan wasa yana ƙunshe da tarin haɗarurra wanda yakan zamto barazana, a wasu lokutan ma ya zamto sanadin rasa rayuka misali, a ce an yi wa wani mummunan duka a ciki, ko a kai, ko dai a wani muhimmin waje da zai iya cutarwa, sannan kuma kasancewar wannan gasa takan ƙunshi ko ya sami halartar mutane daban-daban, faɗa na iya ɓarkewa tsakanin ‘yan kallo, ko kuma waɗanda dama can suna da ‘yar ƙullaliyar gabarsu a qasa, don haka ana haɗuwa sai ɗaukar fansa.

A ɗayan ɓangaren kuma duk saurayin da ke neman aure zai bata jikinsa tas a cikin laka, tun daga fuska har kafafu sannan ya dingi yawo tumvur, yana kewaye mutane ɗauke da ƙatuwar itace. Wannan al’ada suna kiransa ‘Dongo’.

Bayan an kammala gasar, to a nan ne kuma ‘yanmata za su fito suyi ta zaɓen samarin da suke so a cikin waɗanda suka yi nasara a matsayin mazajen aurensu.

Abinci:

Duk da yawan dabbobin da suke kiwatawa, waɗannan mutane ba sa cin nama daga cikin dabbobinsu har sai idan ya kasance akwai wani gagarumin biki ko taro.

Abincin nasu dai sukan sarrafa shi ne ta hanyar tatsar madara daga cikin dabbobin ko kuma jinin dabbobin wanda suke samu ta hanyar yiwa dabbobin rauni. Sannan bayan an tari iya adadin jinin da ake buƙata sai kuma a yi wa dabbar maganin raunin da aka yi ma ta ta hanyar manna ƙarfe mai zafin gaske a jikin ciwon. Masu iya magana dama sun ce abincin wani gubar wani.

Wannan ƙabila ta Suri har gobe tana riqe da al’adunta da ta gada tun iyaye da kakanni ba ta canja ba, duk da sauye-sauyen zamani da ake fuskanta.