Gwamna Lawal ya gwangwaje manoma da kayan aiki a Tsafe

Spread the love

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya raba wa manoman yankin Karamar Hukumar Tsafe kayayyakin aikin gona domin bunkasa harkokin noma a fadin jihar.

Rabon kayan aikin wanda ya guda a ranar Litinin, bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi wajen farfado da harkokin rayuwa bayan wucewar annobar Korona da kuma shirin tada komadar tattalin arziki daukar nauyin shirin FADAMA III.

Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce, Gwamnatin Zamfara ta ware kaso a kasafin 2024 domin gyara madatsan ruwa guda tara da ake da su a yankin Karamar Hukumar Tsafe.

Ya kara da cewa, yayin da yake kaddamar da rabon kayayyakin, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta samar da gurbin aiki sama da 40,000 ga manoma a yankin karamar hukumar.

Haka nan ya ce, Gwamnan ya bayyana cewa Madatsin Ruwa na Yanwaren Daji na da karfin da mutum miliyan biyu za su amfana da shi duk a shekara.

A cewar Gwmna Lawal, “Harkar noma wadda ita ke samar da sama da kashi 70 cikin 100 na karfin tattalin arziki, na ci gaba da zama kashin bayan tattalin arzikinmu.

“Lura da haka ya sa muke da shirin tallafa wa manoma sama da 100,000 a tsakanin kananan hukumomi 14 da jihar ke da su da ingantattun kayan noma a tsakanin shekaru hudu masu zuwa,” in ji Gwamnan.

By Editor