ABDULAZIZ TIJJANI BAKO (PhD)
Umurni na farko da Allah (SWT) ya bai wa Annabi (S.A.W) a Kurani shi ne ya yi karatu (Ikra’ bismi rabbikalladhi khalak: Yi Karatu! Da sunan Ubangijinka, wanda Ya halicci komai da komai). Wannan aya karara ta nuna cewa daya daga cikin abinda ya fi komai muhimmanci ga rayuwar dan’adam shi ne ilimi.
A inda mishkilar take shi ne sau da yawa mutane suna dauka cewa a musulunci idan ana maganar ilimi, kawai zallan ilimin addini a ake magana, wanda hakan kuma kuntata fahimta ne.
Ko shakka babu idan ana maganar ilimi a addinin musulunci ana gabatar da ilimin addini, amma shi ma ilimin zamani ko ilimin boko ko ilimin duniya shi ma wani nau’in ilimi ne da tun daga zamanin Annabi (S.A.W) muhimmancinsa ga al’ummar musulmi ya bayyana. Daga nan zan ja hankalin mai karatu cewa duk inda na ce ilimin boko a wannan wasida, ina nufin ilimin da ba na addini ba.
Lokacin da aka yi yawin badar aka kamo fursinonin yawi ana tunanin yadda za a yi da su, daya daga cikin sharuddan da a ka sanya na fansar fursunonin shi ne duk wanda a cikinsu ya iya rubutu da karatu za a hada shi da wani adadi na yara ya koya musu rubutu da karatu a matsayin fansarsa. Wannan qarara ya nuna muhimmancin samun ilimin da ba na addini ba ga al’ummar musulmi.
Haka kuma Zayd bin Thabit, shi ne daya daga cikin manyan mahaddatan al-Kurani a zamanin Annabi (S.A.W), Annabi (S.A.W) ya ji labarin kaifin basirarsa, wanda hakan ne ya sanya Annabi (S.A.W) ya sa shi ya koyi yaren yahudanci da kuma wani yare na nasara, wanda a ke kira “Syriac Language.” Duka wadannan ilimai na yare ba iliman addini ba ne. Amma saboda muhimmancinsu ga musulunci Annabi (S.A.W) ya sanya daya daga cikin sahabinsa ya koye su.
Duka wadannan misalai suna nuna mana matukar muhimmancin da ke tattare da koyon ilimai wadanda ba na addini ba, amma kuma wadanda za su taimaka sosai wurin inganta rayuwar musulmai.
Imamu Ghazzali, a cikin littafinsa na ihya’ ulumuddeen, ya karkasa ilimi gida-gida: da ilimin addini, da kuma ilimin da ba na addini ba (boko). Sai ya qara da cewa shi ilimin boko ya kasu zuwa ga wanda ya zama wanda ya ke mai kyau, da maras kyau, da kuma la ba’sa. Sannan sai ya kara da cewa ilimi mai kyau din ma kashi-kashi ne.
Akwai wanda ya ke fardu-kifaya ne, wato ya zama wajibi a ce wani rukuni na al’ummar musulmi sun koye shi (kamar ilimin likitanci, da lissafi, da sauransu). Akwai kuma sauran ilimai na boko da yake da matuqar muhimmanci a ce musulmai sun koye su amma ba su zama wajibi ba.
Daga nan za mu gane cewa lallai ilimin boko abu ne mai matukar muhimmanci ga al’ummar musulmai wanda tun daga zamanin Annabi (s.a.w) har zuwa sahabbai da tabi’ai da wadanda suka biyo bayansu suka yi bayani a kan muhimmancinsa ga rayuwar musulmi.
Ko a baya-bayan nan an tambayi malaman Fatawa al-Lajnah ad-Daa’imah a kan falalar ilimin boko, suka yi jawabin cewa lallai idan ana maganar ilimin da ke karawa ba wa kusanci da Allah to ana maganar ilimin addini ne, amma kuma suka kara da cewa shi ma ilimin boko idan an yi shi da kyakkyawar niyya ta amfani da shi ilimin wurin taimakon musulmai da addinin musulunci, to shi ma ilimin bokon zai bai wa mutum falalar samun karin kusanci da Allah (S.W.T).
Kwanakin baya Farfesa Maqari, limamin masallacin Abuja, ya yi wani bayani na zaburar da musulmi su nemi ilimin boko. A wannan zaburarwar ya nuna cewa maganar fifikon ilimi fa yana ta’allaka ne ga abinda al’umma suka fi bukata. Idan a al’umma akwai masu koyar da ilimin addini da yawa sai ya kasance likitoci sun yi karanci, to fa bayar da himma wurin neman ilimin likitanci zai fi muhimmanci ga wannan al’umma fiye da a ce kowa ya raja’a a kan neman ilimin addini.
‘Yan’uwa mu sani cewa addinin musulunci da musulmai suna fuskantar barazana kusan daga kowane vangare na mutanen da musulmai. Arewacin Najeriya na daya daga cikin wurarre mafi kaskanci a fannin ci gaba, sannan mafi shahara a fannin talauci da rashin ilimi a duniya. Bai kuma kamata a matsayinmu na musulmi mu bar kanmu mu zama makaskanta ba. Dole ne mu tashi tsaye mu nema wa ‘ya’yanmu ilimin boko mai karfin inganci in dai muna so mu gan su sun taso cikin kuwwa da izza a tsakaninsu da abokan zamanmu.
Mu tuna Allah (S.W.T) ya umurci Musulmai Surar Aali-Imrana aya ta 200 cewa:
“Ya ku wadanda suka yi imani, Ku yi hakuri kuma ku yi juriya, kuma ku kasance (kodayaushe) cikin shirin ko ta kwana, kuma ku yi takawa, za ku rabauta.”
Sannan kuma suratul Anfal aya ta 60 Allah (S.W.T) ya umurci muminai su kasance masu tattali da tanadi saboda makiyanmu.
A cikin wannan aya ta 60 ta cikin suratul Anfal Allah ya umurci muminai su tanadi dawakai sabosa su tsoratar da makiya. Amma dukkaninmu mun sani cewa a wannan zamanin da muke ciki tanadin dawakai ba zai tsoratar da abokan hamayyarmu ba. Tanadin ilimi da kasaita a takanolaji da kirkire-kirkire, harkar lafiya, harkar noma, harkar jarida, da sauransu su ne za su sanya mutane su riqa shakkar al’umma. Su kuwa wadannan abubuwa ba za su samu ba ba tare da ilimin boko ba.
Kenan idan mun yi duba mai zurfi a kan wadannan ayoyi za mu ga cewa lallai neman ilimin boko a wannan zamanin ba wai kawai abin so ba ne ba ga musulmi. A’a wajibi ne, musamman ga musulmin Arewacin Nijeriya su neme shi su yi kuma zurfi a cikinsa.
Galibin matsalolin da muke fuskanta a Arewa na talauci da kashe-kashe da harkar ‘yan ta’adda, da masu sace mutane, duk suna da alaka da tsananin rashin ilimin boko da ya yi wa al’ummarmu kamun kazar kuku. Don haka babu yadda za a yi lamuranmu su sauya muddin ba mu yi wa kanmu faxa mun rungumi ilimin boko mun karfafe shi a cikin al’ummarmu ba.
Dole ne unguwa-unguwa su kafa kwamitoci da za su tabbatar cewa an yi mai yiwuwa wurin ganin cewa kowane yaro a wannan unguwa ya samu ingantacccen ilimin boko. Akalla a ce babu wani yaro da yake gama firamare ba tare da ya iya turanci da karatu da rubutu ba.
Akwai misalai da yawa wanda wata baiwar Allah mai suna Maman Farha a facebook ta Kawo na muhimmancin ilimin boko ga al’ummar musulmi wanda zan kawo su nan a takaice:
Misalimu dubi kasa ‘yar mitsililiya kamar Koriya ta Arewa. Wannan kasa ba wani karfin tattalin arziki ba ne ba da ita. Amma ta san cewa tana tsakiyar makiya masu qoqarin dakushe ta. Sai ta bayar da himma wurin koyon dabarun kere-keren muggan makamai. Wannan kere-kere su suka jawo cewa duk da valla dokoki da dama da wannan kasa take yi, babu wata kasa da ta isa a yanzu ta tunkari Koriya ta Arewa da zummar wai za ta yake ta ko za ta mamaye ta.
Ko a kasashen musulman idan muka lura za mu ga cewa kasashen da suka mayar da himma a kan ilimin boko da ilimin kere-kere (kamar su Iran da Turkey) ba sa tabuwa. Sai dai a yi ta barazana, amma babu wata kasa mai hankalin da take iya tunkararsu da sunan wai za ta mamaye su.
Yanzu in da a ce kasashen musulmi su ma sun mayar da hankali a kan kere-kere (kamar yadda aka yi a daular usmaniyya da sauran manyan dauloli na musulunci) da ta yaya musulmi za su rika fuskantar irin wannan wulakancin da suke fuskanta a duniya yanzu?
Abdulaziz Tijjani Bako, MBBS, MPH, PhD. Masani ne kuma manazarci a kan al’amurran yau da kullum. Ya runuto ne daga kasar Amurka.
