Bincike: EFCC ta ƙwace fasfo ɗin Betta da Sadiya

Spread the love

A ci gaba da gudanar da bincike da take yi kan zargin almundahana, Hukumar Yaki da Rasahawa ta EFCC, ta kwace fasfo din dakatacciyar Ministar Jinkai da Yaki Talauci, Betta Edu da na wadda ta gada, Sadiya Umar-Farouq.

Ya zuwa hada wannan rahoto, Betta na hannun EFCC na ci gaba da amsa tambayoyi tun bayan da ta kai kanta ofishin hukumar da ke Abuja a ranar Talata da misalin karfe 10 na safe.

Bayanai sun ce binciken zargin wawushe Naira biliyan 44 da ake yi wa Betta ya hada har da wasu majojin bankuna su uku wanda su ma suka gurfana a gaban EFCC a ranar Talata.

Almudahanar da ta ritsa da Edu ta fallasu ne bayan bayyanar wata takardar bayani  da ta nuna dakatacciyar Ministar ta ba da umarnin Akanta-Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein, ya tura  N585m zuwa wani asusu mai zaman kansa mallakar wani mai suna Oniyelu Bridget, wanda ma’aikatar ta ce shi ne jami’i mai kula da aikin raba tallafi ga marasa galihu.

Ministar ta yi ikirarin cewar N585m aka tura kudi ne da aka ware don amfanin kungiyoyin marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun da kuma Lagos, tare da bayyana zargin da ake yi mata a matsayin mara tushe.

A ranar Litinin ne Shugaban Kasa Tinubu ya dakatar da Edu tare da ba da umarni ta mika ragamar ofishinta ga babban sakataren ma’aikatar.

Haka ita ma wadda Edu ta gada, wato  Sadiya Farouq, ba ta kubuta daga binciken na EFCC ba, domin kuwa a ranar Litinin ta hallara ofishin EFCC a Abuja inda ta amsa tambayoyi dangane da binciken badakalar N37.1bn da ake zargin an tafka a zamaninta ta hannun wani dan kwangila mai suna James Okwete.

By Editor