Tare da AMINA YUSUF ALI
Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint manhaja. Yau ma ga mu a wani makon mai albarka. A wannan makon muna tafe ne da bayani a kan yadda matan auren da suke fuskantar cin zarafi a gidan aure musamman a kasar Hausa.
Inda za ka ga cewa, mace ana cin zarafinta, ana hana ta abinci, da sauran hakkokinta na aure ga uwa uba kuma duka da wulakanci. Amma ta kafe ta hakura ta zauna a gidan. Me yake kawo hakan? Kuma meye mafita?
Yawanci sukan dauki matakin hadiye komai su cigaba da rayuwa a haka. Amma abin tambayar shi ne, anya hakan shi ne mafita? Idan ba shi ba ne mafita, to mecece sahihiyar mafitar?
ZaN warware muku zare har abawa kuma mu fede muku biri har wutsiya a wannan rubutun. A sha karatu lafiya.
Mai karatu in dai ya fito daga yankin qasar Hausa ba zai kasa sanin cewa cin zarafi da tauye hakkin mata da wulakanta su wata babbar matsala ce da ta addabi yankin ba.
Kuma suna daga dalilan da sukan kawo yawaitar mace-macen aure. Idan kuma auren bai mutu ba a yi ta shan wuya iya wuya. Wani zubin mutane suna ganin baiken matar da take cikin irin wancan auren na cin zarafi. Suna ganin me zai hana ba za ta kama gabanta, sawunta a likkafa ba kawai ta wuce wajen bs?
To babbar matsalar irin wannan auren ya fi komai wahalar bari. Ga shi tana shan wahalar. Ku da kuke gefe kuna tausaya mata, kuna jiye mata ciwon abin, ita kuma tana zaune da abinta. Ga wasu daga cikin dalilan da suke sa mata zama a gidan auren da ake cin zarafinsu ko ake tauye musu hakkinsu:
Dalili na farko shi ne, wasu matan ko da sun yi niyyar kama gabansu, sai mazan su hana su. A yi, a yi su rabu da su, su ki. Wani ma har danganawa da kotu ake yi amma ba zai saki ba. Sai dai a yi ta tafka shari’a. Ya gwammce ya bi dukkan wasu hanyoyi da matar ba za ta samu nasara ba. Kuma da ma mazan da ba a jin dadinsu sun fi kowa kin yin saki.
Wani har malamai zai shiga ya yi ta addu’a don ya samu ya kafe ta. Shi dai ta zauna ya cigaba da muzguna mata. Abinda bai gane ba, da a ce dukiya da karfin da yake amfani da su, da zai juya su izuwa kyautata mata da watakila da ta so zama da shi ma tsakaninta da Allah. Mace fa idan ka kyautata mata ka gama da ita.
Na biyu, ‘ya’ya. Mun riga mun sani mata abinda suke fara sakowa a gaba kullum shi ne yaransu. Idan miji yana azabtar da mace, ko da ta yi niyyar guduwa don sama wa kanta lafiya, to ba ta iyawa saboda tunanin za ta bar su a cikin wahalar da ta guje wa kanta din. Ko ma wasu wahalhalun da za su iya tasowa a gaba. Wata kuma tana tausaya musu kada su taso ba tare da uba ba, ko uwa. Ba sai na yi dogon bayani a kan matsalolin da ‘ya’yan da mace ke fuskanta a kasar Hausa ba. Da kuma ‘ya’yan da suka taso a hannun matar uba ba.
Na uku, akwai matsala ta iyayen matar ko wani nata mai fada a ji. wasu iyayen su suke tilasta ta, ta koma duk lokacin da ta yi yunqurin guje wa azabar da take ciki. Wasu iyayen har cewa suke idan ta fito ba su, ba ita. Ko kuma za su tsine mata idan ta fito.
Shi ya sa sai ta zama ba ta da zavi sai dai ta zauna a cikin azababben auren. Ko da yana hana ta abinci, iyayenta sukan hada mata kayan abinci su sake tura ta ta koma. Kuma abin takaicin wani auren ma duk da hakan sai ya mutu. An gudu dai ba a tsira ba. Gara ma da kiransa aka yi, aka nusar da shi hakkin nasa.
Na hudu, akwai al’ummar da muke ciki. Ita ma ta bayar da gudunmowa sosai. Kina fitowa daga aure, laifinki ne, mugun hali gare ki. Ba ma idan kin yi auren kin fito fiye da sau daya. Al’ummarmu ta yi kaurin suna wajen tsangwamar bazawara. Kuma an riga an yarda da ma ba a auren dadi wai dole aure zaman haquri ne. Ko ina aka samo wannan? Wannan zai sa ta yi ta tsoron fitowa don kada a kalle ta a mara hakuri kuma mara kirki.
Na biyar, akwai so. Hausawa sun ce, ‘so hana ganin laifi’. Tsakanin kuma mata da miji, sai Allah. Idan mace na son namiji duk irin cin zarafinta da zai ko ya tauye mata hakki, tana iya shanyewa da kau da kai, tare da yi masa uzuri. Wata har dora ma kanta laifi take a zuciyarta don ta kare abin son nata.
Wata ko ta fusata ta tafi din, haka za ta hakura ta sake dawowa wajen masoyin nata, shi kuma ya cigaba daga inda ya tsaya a cin zarafinta. Ba ma idan ya iya ba ta hakuri da yin tausasan lafuzza ko ya iya yi mata wata kyauta a matsayin toshiyar baki. Duk lokacin da ya vata mata rai. Wata duk dukan da ya yi mata, in dai ya iya rarrashi, a take za ta yafe. Za mu cigaba a mako na ga ba a idan rai ya kai.
Na gode masoya Allah ya bar zumunci.
