Gwamna Raɗɗa ya buƙaci Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa da ta kammala aikin titin Katsina zuwa Kano

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, yayi wannan roko ne a lokacin da ya kai ziyara a ofishin Ministan Ma’aikatar Ayyuka, Sanata David Umahi, a ranar Talata, 9 ga watan Janairu 2023 a Abuja.

A lokacin ziyarar, Gwamnan ya samu rakiyar Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Katsina, Injiniya Sani Magaji, Alh Abdullahi Turaji da sauran su.

Gwamna Radda ya jaddada wannan bukatar ne, inda ya yi nuni da cewa, duk da cewa an bayar da kwangilar gina hanyar a shekarar 2019, amma aikin nayin tafiyar hawainiya. Ya kuma bayyana muhimmancin sa hannun gwamnati bisa la’akari da muhimmancin hanyar. Duk da cewa Gwamnan yayi la’akari da cewa an kammala kaso 68% cikin Jihar Kano, ya nuna damuwarsa cewa kashi 27% na Katsina ne kawai aka aiwatar.

Bugu da kari, Gwamna Radda ya nemi taimakon ministan wajen gaggauta gyaran hanyar Zaria/Danja/Kafur/Malumfashi, wanda hukumar ta FERMA ke gyarawa a halin yanzu. Ya bukaci a saka aikin a cikin kasafin kudin shekarar 2024, inda ya ba da tabbacin gwamnatin jihar ta himmatu wajen biyan diyya ga masu filayen da aikin hanyar Kano zuwa Daura zuwa Kongolom ya shafa.

A nasa jawabin, Ministan Ayyuka, Cif David Umahi, ya taya Gwamna Radda murnar zaɓen da ya lashe, tare da ba shi tabbacin goyon bayan ma’aikatar wajen kammala dukkan ayyukan gwamnatin tarayya a Katsina.