Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (III)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A makon jiya muka cigaba da kawo wa masu karatu takaitaccen tarihin sarakunan Fulani wadanda suka fara mulkin kasar Kano tun daga jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo kawo yau. To, a yau za mu cigaba gaba inda muka tsaya.

A zamanin Sarki Alu an samu sa-in-sa a tsakanin Ningi da Kano. Amma saboda Sarki Danyaya yana jin tsoron Sarki Alu sai ya zama ba a gwabza yaki ba.

Sannan dai a zamanin Sarki Alu ne gaba ta tsananta a tsakanin Kano da Hadeja. A wannan zamani Sarki Muhammadu ne ya ke sarautar Hadeja.

Sarkin Kano Alu shi ya gina garuruwan Fajewa da Dando da Magami da Bura da Kwajali da Musa duk a Kudancin Kano a zamaninsa.

Daga karshe, Sarkin Kano Alu ya tafi kai caffa Sakkwato Turawa suka zo suka ci Kano. Wannan labari na shigar Turawa Kano ya iske sarki Alu a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta dawowa Kano shi da jama’arsa da suka hada da sarakuna da hakimai da fadawa da lifidai da sauransu. Da labari ya same su, jama’arsa sun ba shi shawarwari kamar haka: “Kodai ka tsaya mu yi faxa da Turawa, ko kuma ka nemi sulhu da su”. Wadansu kuma suka ce a’a, ya koma Sakkwato wanda kuma hakan ce ta faru. Sarki Alu da wadansu jama’a suka koma Sakkwato. Wadansu kuma ciki har da Wambai Abbas da Waziri Ahmadu da wadansu jama’ar sai suka cigaba da tafiya Kano.

Da wannan ayari ya iso Kwatarkwashi sai ya yada zango. A wannan zango nasu sai suka hadu da Turawa. Zatonsu Damagarawa ne saboda haka sai suka far musu da yaki. A karon farko sai aka kashe Waziri Ahmadu, da dansa da dan morinsa. Haka yaki ya kare. Wambai Abbas da sauran jama’a suka dawo Kano.

A lokacin da Wambai Abbas ke kan hanyarsa ta komawa Kano, sai Turawa suka tura aka tarbe shi. Wambai Abbas da ayarinsa sun isa Kano ranar Juma’a. Sun shiga Kano ta Kofar Kansakali. Kafin shigarsu Kano sai da Turawa suka caccaje kayayyakinsu suka kwace dukkan makamansu. Sarki Aliyu Mai Sango, ya rasu bayan ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara tara da wata tara.

Muhammadu Abbas, 1903-1919 Miladiyya:

Sarki Muhammadu Abbas shi ne Sarki na 51 a jerin Sarakunan Kano, kuma Sarki na 8 a jerin Sarakunan Fulani, har wa yau kuma shi ne Sarki na farko da Turawa suka fara nadawa.

Sarki Muhammadu Abbas mutum ne jarumi, kuma mai fada da cikawa ko kuma ana iya cewa mutum ne kaifi daya. Ya kasance Sarki mai hakuri da jama’arsa.

Sarki Abbas ya yi mulki tare da Turawa, saboda haka hakimansa suka samu dama ta dalilin hakurinsa da kawaicinsa suna iya yin magana kai-tsaye da Turawa, har sai da ta kai munafunci ya fara gudana a tsakanin Turawan nan da wadansu daga cikin hakiman Sarki Abbas. Irin wannan lamari na tsaka da faruwa sai Allah Ya kawo wani Bature mai suna Mista Temple, shi ya taka wa wannan al’ada birki. Ya samar da kyakkyawan tsari, ya yanka wa sarakuna da sauran ma’aika albashi. A zamanin Sarki Abbas ne aka yi wani gagarumin taron sarakuna, Gabas da Yamma, Kudu da Arewa a 1912. A zamanin Sarki Abbas ne aka gina wasu kasuwanni a Kano. Sannan a zamaninsa ne a 1910 aka gina wata makaranta a cikin Nasarawa wacce a yanzu ta koma Gidan Danhausa.

Sarki Muhammadu Abbas ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara 16. Ya rasu a 1919. An binne shi a gidansa da ke Nassarawa.

Usman dan Abdullahi, 1919-1928 Miladiyya:

Sarki Usman dan Abdullahi, wanda ake yi wa lakabi da Usman II. Shi ne Sarki na 52 a jerin Sarakunan Kano, kuma Sarki na 9 a jerin Sarakunan Fulani. Haka kuma shi ne Sarki na biyu da Turawa suka nada.

An nada Sarki Usman ne bayan ya rike Kano na tsawo kwana 40. A lokacin da ya samu sarautar tsufa ta zo masa. A wannan lokaci yana da shekara 76 a duniya.

A zamanin Sarki Usman II, an yi gagarumin taron sarakunan Arewa sakamakon zuwan dan Sarkin Ingila wanda ya zo a jirgi. Saboda haka a zamanin Sarki Usman II ne jirgin sama ya fara zuwa Kano. An yi wannan taro a 1925. A kuma zamanin Sarki Usman II aka fara aikin ruwan famfo da na wutar lantarki da kuma gina wasu asibitoci da kuma babban ofishi a cikin birnin Kano. Amma ba a kai ga kammalawa ba rai ya yi halinsa.

Sarki Usman II, ya sarauci Kano na tsawon shekara bakwai da wata biyu a cikin yanayin tsufa da rashin lafiya. Ta-ci-ba-ta-ci-ba, haka ya yi mulkin. Allah Ya jikansa da rahama, amin.

Abdullahi Bayero dan Abbas (1926 zuwa 1953) Miladiyya:

Sarki Abdullahi Bayero shi ne Sarki na 53 a jerin Sarakunan Kano kuma Sarki na 10 a jerin Sarakunan Fulani. Sannan kuma Sarki na 3 da Turawa suka nada. An nada Sarki Abdullahi Bayero a matsayin Sarkin Kano ne lokacin yana Ciroman Kano. Shi ne farkon Ciroman Kano da ya zama Sarki. Sarki Abdullahi Bayero mutum ne mai hakuri da kuma tattalin jama’arsa.

A zamanin Sarki Abdullahi aka kammala aikin ruwan famfo da aka jawo daga Kogin Calawa zuwa Gwauron Dutse sannan aka rarraba shi zuwa unguwanni da gidaje. Sannan a zamaninsa aka kammala aikin wutar lantarki. A zamaninsa aka kammala ginin Asibitin Shahunci. Sannan a zamaninsa aka gina Makarantar Midil ta Kano wadda ta koma Kwalejin Rumfa. Wannan makaranta tana nan a kan titin zuwa Jami’ar Bayero daga Gidan Murtala. Tana nan tana kallon katangar badala da ke tsakanin Sabuwar Kofa da ofar Dan’agundi daidai bakar lamba.

Sannan a lokcinsa aka gina Makarantar Koyon Sana’o’i ta Kofar Nasarawa. Sarki Abdullahi shi ya sa aka yi ta ciccike kududdufan da ke cikin birnin Kano saboda kiwon lafiya. Sannan a lokacinsa aka gina Makarantar Aikin Shari’a da ta Koyon Aikin Shari’ar, wato ‘Judicial’ da kuma ‘Law school’. Ita Judicial ita ce ta koma Makarantar Koyon Harshen Larabci (School for Arabic Studies -SAS) da ke Kwalli a halin yanzu.

Sarki Abdullahi Bayero ya mulki Kano na tsawon shekara 27.