Gwamna Lawal ya raba wa manoma kayan aiki a shiyyar  Zamfara ta Arewa

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ci gaba da aiwtar da shirinsa na raba wa manoman jihar kayayyakin aikin gona inda a wannan karon shirin ya yada zango a shiyyar Zamfara ta Arewa.

A ranar Alhamis ta makon jiya aka kaddamar da rabon kayayyakin a Gidan Gona da ke yankin Karamar Hukumar Shinkafi.

Rabon kayayyakin in ji Mai magana da yawunsa, bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi wajen tada komadar tattalin arziki bayan wucewar annobar Korona.

Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa za a kaddamar da wannan shiri a mazabun sanata guda ukun da jihar ke da su.

Ya kara da cewa, a ranar Larabar da ta gaba aka kaddamar da rabon kayayyakin a shiyyar Zamfara ta Tsakiya a Gusau, babban birnin jihar.

Ana sa ran wadanda za su ci gajiyar shirin su samu tallafin kayan aiki da suka hada da magungunan kashe kwari da ciyayi da kuma irin shuki mai inganci har na tsawon shekara hudu.

A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar na ware kadarori domin sha’anin noma da rage asarar abinci a jihar baki daya.

Kalamansa: “Da rahamar Allah (SWT), a halin yanzu hankalinmu ya karkata ne kan sakamako na 2, karkashin shirin FADAMA III, wanda burinmu shi ne kara samar da wadataccen abinci, musamman ga marasa galihu.”

Ya kara da cewa, samar da ababen more rayuwa a yankunan karkara na da matukar tasiri wajen bunkasa harkokin noma, don haka ya ce “gwamnatina ta dori aniyar gina hanyoyi masu tsayin kilomita 70, kasuwanni guda 40 masu dauke da shaguna 4,000” a yankunan karkara da ke sassan jihar.