Gwamnan Kano ya nemi al’umma a dage da addu’ar zaman lafiya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci al’ummar jihar da su dage da addu’ar samun zaman lafiya ga Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya yi wannan kira ne a cikin saƙon taya murnar bikin maulidin Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) na bana wanda ya isar ta bakin Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta jihar, Baba Halilu Dantiye, MON wanda ka raba wa manema labarai a jihar.

Albarkacin bikin maulidin na bana, Gwamnatin Jihar ta ayyana Laraba, 4 ga Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin maulidin wajen wanzar da kyawawan karantarwar Manzo S.A.W kamar yadda ya koyar a halin rayuwarsa.

Kazalika, ya roƙi Allah da Ya kuɓutar da al’umma daga wahalhalun rayuwa da ake fuskanta, kana Ya albarkaci daminar da ake ciki da ma kaka mai zuwa.