Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta yanke shawarar yin amfani da rahoton yi wa ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya garambawul na kwamitin Steve Oronsaye, domin a rage yawan kashe kuɗaɗe wajen tafiyar da ayyukan gwamnati.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a ƙarshen taron majalisar a ranar Litinin, a Abuja.
Idris ya ce wasu Ma’aikatun da Sassa da Hukumomi da Cibiyoyi za a rushe su, za a haɗe wasu da wasu, wasu kuma za a maida su cikin hukumomin gwamnati da suka cancanta.
Sai dai Idris ya ce dalilin yin hakan shi ne don gwamnati ta rage kashe kuɗaɗe, amma ba don a kori ma’aikata ba.
Ministan wanda ya ce za a ji adadin yawan ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa na da daɗewa ba, ya ƙara da cewa an kafa kwamitin da zai zartas da wannan aiki.
Dangane da batun masu tafiya yajin aiki, Idris ya ce gwamnatin tarayya ta cika fiye da kashi 85 bisa 100 na yarjejeniyar da ta cimma da qungiyar qwadago ta ƙasa (NLC), a cikin 2023.
Ministan ya ƙara da cewa shugabanin ƙungiyar ƙwadago su dubi irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen ganin ta magance qalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.
Ya ce bai kamata ‘yan ƙwadago su bayar da wata kafar da waɗanda ba su yi wa ƙasar nan fatan alheri ka iya kawo ruɗani a wannan mawuyacin halin da ake ciki ba.
Haka nan kuma Majalisar Zartaswa ta amince a ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin marasa galihu a ƙarƙashin shirin NSIP.
Shi kuwa Ministan Kuɗaɗe, Wale Edun, cewa ya yi za a ɗauki matakan da suka dace domin tantance waɗanda suka cancanta su ci gajiyar tallafin.
Ya ce dukkan waɗanda za su ci gajiyar tallafin za a tantance su ne ta hanyar lambar sirri ta asusun bankin su (BVN) da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN), sai kuma lambar asusun bankin su, ko da bayan an biya su kuɗaɗen ne.
Edun ya ce sake farfaɗo da shirin bayar da tallafin kuɗaɗen ya zo daidai ne lokacin da wannan gwamnati ke ƙara azamar magance ƙalubalen tsadar rayuwa da marasa galihu ke fuskanta.
Ya ce gidaje miliyan 12 ne za su ci moriyar shirin, kuma nan ba da daɗewa ba ne za a fara tura masu Naira 25,000 daga shirin NSIP.
