Gwamnatin Zamfara ta yi wa marasa lafiya 2,213 magani kyauta

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta ce ta yi wa ‘yan jihar su 2,213 magani kyauta albarkacin shirinta na kula da lafiya kyauta da take gudanarwa.

Gwamnatin ta ce kawo yanzu ta kammala kashi na uku na shirin wanda aka samar domin kyautata lafiyar ‘yan jihar musamman masu fama da rashin lafiya.

Wannan bayani na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce kashi na uku na shirin ya gudana ne daga ranar 23 zuwa 25 na Fabrairun 2024.

“Gwamnatin Gwamna Lawal ta samar da shirin ba da magani kyauta domin kula da marasa galihu. Shirin na ba da magani kyauta ga masu fama da lalurori da suka haɗa da hakiya, ƙaba, yoyon fitsari” da sauransu, in jin sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Kawo yanzu shirin ya yi wa mutum 2,213 magani a sassan ƙananan hukumomi 14 da jihohin ke da su.

“Kawo yanzu, shirin ya yi wa masu fama da wani tsiro mutum 876, an cire wa mutum 931 hakiya, sannan an yi wa mutum 84 maganin yoyon fitsari (VVF).

“Wuraren da aka gudanar da shirin sun haɗa da Babban Asibitin Gusau, Babban Asibitin Sarki Fahad, Asibitin Ƙwararru na Yariman Bakura, sannan masu lalura ta musamman za a tura su Babban Asibitin Tarayya da ke Gusau.”

By Editor