Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Hisbah, Sheikh Daurawa ya ajiye muƙaminsa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Hukumar Hisbah a Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da ajiye muƙaminsa a matsayin Babban Kwamandan Hisbah, tare da nuni davrashin ƙwarin gwiwa daga ɓangaren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Daurawa ya ce duk da ƙoƙarin da yake yi wajen kyauta tarbiyya a jihar a matsayinsa na shugaban Husbah, amma cewa ya karaya da yanayin kamalaman gwamnan.

Faifan bidiyonnya ya yaɗa a shafinsa na soshiyal midiya, Malamin ya ce, “Yanzu haka ina Jihar Kaduna ina ganawa da ‘yan majalisa ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar don tattauna aiwatar da dokar yin gwaji kafin aure a Kano kwatankwacin yadda abin yake a sauran jihohi.

“Sai dai na fuskanci kalaman rashin ƙwarin gwiwa daga Kano duk da ƙoƙarin da nake yi a Hisbah wajen kyautata tarbiyya.

“Mun sami ‘yan Kannywood da masu yin TikTok inda muke ɗora su kan turbar da ta dace har da tallafa ma wasunsu da kuɗi. Hatta ita ma Murja na shawarce ta

“Sai dai waɗanda suka bijire wa shawarwarinmu sun fuskanci hukunci.

“Amma ina na mai bai Mai Girma Gwamna haƙuri bisa ransa da ya ɓaci, a yi haƙuri ina mai bayyana murabus ɗina daga muƙamin da ya naɗa ni a Hisbah, ina yi masa fatan alheri a shugabancinsa,” in ji Daurawa.

Gwamna Yusuf ya nuna rashin gamsuwarsa game da yadda Hisbah ke gudanar da harkokinta ƙarƙashin shirinta mai taken ‘operation kau da baɗala’ a faɗin Kano.

‘Operation Kau da Baɗala’ shiri ne da Hisbah ta ƙirƙiro da zummar yaƙi da rashin ɗa’a a Jihar Kano.