MOPPAN ta nuna damuwa kan murabus ɗin Kwamandan Hisba

*Ta buƙaci Daurawa ya sake nazari kan matakin da ya ɗauka

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN) ta nuna damuwarta kan ajiye muƙami da Sheikh Aminu Daurawa ya yi a matsayin Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano.

MOPPAN ta ce Daurawa ya ajiye muƙamin nasa ne bisa dalilin rashin ƙwarin gwiwa daga ɓangaren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a mai ɗauke da sa hannun Sakataren Hulɗa da Jama’a na Ƙasa, Al-Amin Ciroma.

MOPPAN ta bakin Shgugabanta na Kasa, Habibu Barde, ta ce tana sane da kuskuren da Hisba ta yi wanda Gwamna Kabir ya nuna damuwarsa a kai, amma duk da haka ta ce ta yi amanna da haɗin kai da daidaiton da ke Hukumar Hisba don amfanin al’umma.

Daga nan Al-Amin Ciroma ya yi kira ga shehin malamin da ya sake nazari kan murabus din da ya yi sannan ya ci gaba da aikinsa a matsayin shugaban hukumar ta Hisbah.

Sanarwar ta ce, “MOPPAN na jaddada muhimmancin tasirin Sheikh Daurawa a matsayinsa na fitaccen malami tare da ƙarfafa masa kan kada ya juya baya daga aikin gyara tarbiyya a cikin al’umma.

“Ƙungiyar na sane da girman lamarin tare da kira da a fahimci juna tsakanin Sheikh Daurawa da Gwamnatin Kano.”

MOPPAN ta ƙara da cewa, ta yi ammana kan cewa tattaunawa da fahimtar juna na da matuƙar muhimmanci wajen daidaita ɓangarorin biyu.

Haka nan, ta ce lallai Hisbah na taɓukawa a ƙarƙashin jagorancin Malam Daurawa saboda an shaida yadda ake samun raguwar baɗala a cikin al’umma dalilin jagorancin da yake yi wa Hisba.

A ranar Juma’a Sheikh Daurawa ya sanar da murabus ɗinsa a matsayin Kwamandan Hukumar Hisba bisa dalilin rashin ƙwarin gwiwa daga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.