Gwamnati ta umarci Shugaban Hukumar Imigireshan, Isah Idris ya yi ritaya

Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, ya umarci Shugaban riƙo na Hukumar, Isah Idris, da ya gaggauta yin ritaya daga aiki ya zuwa 24 ga Afrilun 2023, ko kuma kafin wannan rana.

Sanarwar da Kwamitin ya fitar wadda jaridar News Point Nigeria ta samu leƙawa, ta nuna ƙarewar wa’adin shekara ɗaya da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa Idris a bakin aiki.

Kwamitin ya umarci CGI Isah Idris da ya yi murabus kana ya miƙa ragamar jagorancin hukumar ga Mataimakin Kwanturola Janar mafi daɗewa a aiki.

Sanarwar mai ɗauke da kwanan wata 17 ga Afrilu, 2023 da lamba CDCFIB/APPT.CG&DCG/61/VOL.IV/74, na ɗauke ne da sa hannun Sakataren Kwamitin Gudanarwar, Obasi Edmond, bisa umarnin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola.

Gwamnatin Tarayya ta yaba wa Isah Idris dangane da gudunmawar da ya bayar ga cigaban hukumar yayin jagorancinsa.

Idris ya zama Shugaban riƙo na hukumar ne a Satumban 2021 biyo bayan murabus da tsohon CGI, Muhammed Babandede, ya yi.

Bayanai sun ce lokacin yin ritayar Idris ya kai bayan da ya cika shekara 60 da haihuwa a ranar 24 ga Afrilun 2022 kamar yadda dokar aikin gwamnati ta tanadar, amma sai Shugaba Buhari ya tswaita masa wa’adi da shekara guda.