Gwamnatin Kano ta dakatar da shugaban hukumar sakandare da na makarantar lafiya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Kwalejin Lafiya ta Health Technology Bello Ɗalhatu, da Mai riƙon Shugabancin Hukumar Lura da Makarantu Sakandire ta jihar (KSSMB), Malam Ado Tumfafi.

Hakan na cikin wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya fitar.

Sanarwar ta ce an dakatar da su ne saboda zargin karɓar kuɗaɗe daga ɗalibai da kuma wasu ƙarin zarge-zarge.

Sanarwar ta zargi Tumfafi da karɓar kuɗin ɗalibai da sanya wa malamai harajin ba gaira ba dalili da sunan kuɗin fom ɗin ƙarin girma da sauransu.

Gwamnatin, ta kuma umarci manyan sakatarori na ma’aikatun ilimi da lafiya da su kafa kwamitin bincike a kan mutane biyun.

Gwamnatin Kano ta ce ba za ta sassauta wa duk wani shugaban hukuma da ya yi amfani da ofishinsa wajen cuzgunawa jama’a ba.

Haka kuma, ta yi alƙawarin ƙwato wa iyayen ɗalibai da malamai da aka karɓi kuɗinsu haƙƙoƙinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *