Gwamnatin Nasarawa za ta cigaba da hukunta masu harƙar ma’danai ba bisa ƙa’ida ba a jihar

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya

Gwamnatin jihar Nasarawa tace zata cigaba da tsare tareda hukunta masu haƙar ma’danai ba bisa ka’ida ba a jihar.
Kwamishinan ma’aikatan muhalli da albarkatun ƙasa na jihar honorabul Kwanta Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattauna da manema labarai a ofishin sa dake Lafia.


Yace ba shakka hakan haƙƙi ne daya rataya a wuyar gwamnatin jihar ta tabbatar tana kare duka ma’adanai da sauran kaddarorin jihar musamman Idan akayi la’kari da yadda wasu Ke shigo jihar daga wasu jihohin daban don haƙar ma’adanan ba bisa ƙa’ida ba Kuma basa karban lasisin aikin.


Honorabul Kwanta Yakubu ya kuma yi amfani da damar inda ya musanta wani zargi da Wani Mai harkar ma’adanan daga jihar Filato yayi cewa bayan ya cika sharudan hakar ma’danan a jihar yama fara aikin sa sai daga baya gwamnatin jihar ta dakatar da shi ta karbi wajen daga gun sa inda yace, hakan ba gaskiya bane gwamnatin jihar ta karbi wajen daga gun sa ne bayan ta Gano cewa bai da lasisin, kuma bai cika sharudan hakar ma’danan a jihar ba, inda yace tuni gwamnatin jihar ta yanke shawarar taka wa ire-iren sa birki.