Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Cocin Katolika domin magance ƙalubalen Nijeriya – Akume

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya tabbatar da aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Taron Limaman Cocin Katolika na Nijeriya (CBCN), sauran ƙungiyoyin addinai, cibiyoyin gargajiya, ƙungiyoyin fararen hula da kuma kamfanoni masu zaman kansu domin magance manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Sanarwar da Mai Ba SGF Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Yomi Odunuga, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa Akume ya yi wannan bayani ne bayan wata ganawa da Shugaba Tinubu ya yi da shugabannin CBCN.

Akume ya ce, magance matsalolin Nijeriya ba zai yiwu ba sai an samu tattaunawa mai ma’ana da ba da shawarwari na gaskiya daga dukkan masu ruwa da tsaki.

Ya ce al’ummomin addinai, cibiyoyin gargajiya, ƙungiyoyin fararen hula, kamfanoni masu zaman kansu da kuma ‘yan ƙasa na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kan al’umma da bunƙasa ci gaban ƙasa.

Akume ya bayyana cewa Ofishin SGF zai ci gaba da tuntubar shugabannin Cocin Katolika da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Majalisar Haɗin Kan Addinai ta Nijeriya (NIREC), domin ƙarfafa gina zaman lafiya da hana rikice-rikice.

Ya kuma yaba da gudummawar Cocin Katolika wajen bunƙasa ilimi, kiwon lafiya, ayyukan jin ƙai da jagoranci na ɗabi’a a Nijeriya.

Dangane da tattalin arziki, Akume ya amince cewa ‘yan Nijeriya na fuskantar matsin rayuwa, amma ya ce hakan na ɗan lokaci ne, yana mai jaddada cewa sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na da nufin gyara matsalolin tattalin arziki da dawo da daidaito.

Ya lissafa wasu muhimman matakan da gwamnati ta ɗauka da suka haɗa da zuba jari a manyan hanyoyi da layukan dogo, ƙarfafa noma ta hanyar samar da kayan aiki da tallafi, inganta wutar lantarki, da bunƙasa fannin lafiya tare da samar da ayyukan yi.

A cewarsa, alamomin tattalin arziki na nuna ci gaba, ciki har da daidaituwar kasuwar canjin kuɗaɗe, raguwar hauhawar farashi da kuma ƙaruwa da amincewar masu zuba jari.

Ya ce shirye-shiryen gwamnati kamar NELFUND, Shirye-shiryen Tallafin Jama’a, Credit Corps da kuma tallafin kuɗi kai tsaye ga masu ƙaramin ƙarfi za su taimaka wajen rage wa al’umma raɗaɗin sauye-sauyen tattalin arziki.

Game da tsaro, Akume ya ce gwamnati na ci gaba da faɗaɗa tsarin tsaro ta hanyar kafa sabbin rundunonin soji a jihohin Benue, Kwara, Taraba da Edo, tare da inganta tattara bayanan sirri, dabarun aiki, ɗaukar ma’aikata, amfani da fasaha da kula da jin daɗin jami’an tsaro.

Dangane da batun dimokuraɗiyya kuwa, Akume ya musanta zargin cewa gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

Ya ce gwamnatin Tarayya na ci gaba da mutunta kundin tsarin mulki, bin doka da kuma tabbatar da ‘yancin Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), yana mai cewa rajistar jam’iyyun siyasa 21 da INEC ta yi shaida ce ta wanzuwar dimokuraɗiyya da tsarin jam’iyyu masu yawa a ƙasar.

Ya bayyana ganawar Shugaba Tinubu da shugabannin Cocin Katolika a matsayin mai cike da girmamawa da tattaunawa mai amfani, inda aka tattauna batutuwan tsaro, matsin tattalin arziki, ilimi, sahihancin zaɓe da kuma ‘yancin addini.

Akume ya ce ko da gwamnati da Cocin Katolika ba su yi daidai kan kowace manufa ba, suna da buri guda na ganin kowane ɗan Nijeriya ya rayu cikin zaman lafiya, mutunci da kyakkyawan fata.

By ukarofi

Leave a Reply