Gwamnatin Tarayya za ta fara ba wa maza hutun jego na kwanaki 14

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Larabar nan a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ƙarƙashin shugabancin Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Yemi Osinbajo, sun amince da dokar da ta ba da dama ga iyaye maza waɗanda iyalansu suka haihu, hutun jego domin su ma su samu su ƙara shaƙuwa da jaririn da aka haifa ko ɗan goyon da aka ɗauko.

Shugabar Ma’aikata na Tarayya, Dakta Folasade Yemi – Esan ce ta bayyana hakan a ƙarshen zaman majalisar zartarwar wanda ake gudanar da shi a ƙarshen kowane mako. Wanda aka gudanar da shi a ɗakin taro na Matar Shugaban Ƙasa wanda yake a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shi ma Ministan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa, wannan hutu za a dinga ba da shi ne ga angwayen ƙarni, wato waɗanda matansu suka haihu.

Ita ma Dakta Folasade ta ƙara da cewa, yana da matuƙar muhimmanci yaro ya soma sabawa da mahaifinsa a ranakun farkon rayuwarsa kamar yadda yake fara sabawa da sauran mutane.