Majalisar Dattawan Najeriya ta nemi Buhari ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda

Daga AMINA YUSUF ALI

Majalisar Dattawan Najeriya ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ‘yan fashi da ɓata-garin dake daji da suka addabi yankin arewacin ƙasar a matsayin ‘yan ta’adda, tare da ƙaddamar da yaƙi a kansu.

‘Yan majalisar sun bayyana haka ne a yayin zaman majalisar a ranar Larabar nan da ta gabata. Sannan sun ƙara da cewa, ya kamata kuma a ba da umarni jami’an tsaro su kama su, a gurfanar da su, tare da gaggauta yi musu hukuncin da ya dace da su.

Wannan batu yana ƙunshe ne a cikin wani wani ƙudiri da ɗaya daga cikin ‘yan majalisar, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir mai wakiltar Sokoto ta Gabas ya gabatar a zauren majalisar. Inda ya samu goyon bayan wasu sanatocin guda takwas.

Sanata Gobir ya yi jan hankali a kan wani hari na baya-bayan nan da ɓata-garin suka kai zuwa sansanin sojoji a Sokoto a ƙarshen makon da ya gabata. Inda aka hallaka jami’an sojoji har guda 16 daga hukumomin tsro daban-daban na ƙasar nan.

A cewarsa idan ana rasa irin waɗannan jami’an tsaro a lokaci guda, to watarana za a wayi gari a kasa samun adadin jami’an tsaron sa ake buƙata don gwabzawa da masu ta da tarzoma a ƙasar.

“A halin yanzu ata gari da dama sun yo ƙaura daga zamfara sun dawo ƙananan hukumomin Sabon-Birni da Isa da suke a Jihar Sokoto domin matakin yaƙi da su da ake yi a Zamfara” Inji shi.

Sanata Gobir ya ƙara da cewa, shi kansa salon da ake bi don yaƙar ɓata-garin a zamfara ba tsari ne mai kyau ba. Bai kamata a ce a Zamfara ka]ai ake yi ba. Ya kamat a ce an kai hari dukkan wuraren da aka san miyagun suna iya samun mafaka.