Hajjin 2026: Gwamnan Kano ya naɗa Sarkin Gaya a matsayin Amirul Hajj

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗa Sarkin Gaya, Mai Martaba Alhaji Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin Amirul Hajj na jihar domin jagorantar aikin hajjin shekarar 2026.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an nada Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, a matsayin mataimakin Amirul Hajj.

Gwamnatin jihar ta ce Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano za ta bai wa Amirul Hajj da mataimakinsa cikakken hadin kai domin tabbatar da gudanar da aikin hajjin cikin nasara da kwanciyar hankali.

Hakazalika, gwamnatin ta yi wa Amirul Hajj, mataimakinsa da ma’aikatan hukumar alhazai fatan samun nasara a aikin hajjin bana, tare da addu’ar Allah Ya karbi ibadar dukkan maniyyata tare da dawo da su gida lafiya.

By ukarofi