Hana Ighalo wakiltar Nijeriya: Eguavoen ya mayar da martani ga Al-Shabab

Daga WAKILINMU

Kocin riƙon ƙwarya na Super Eagles, Augustine Eguavoen, ya ce, yana da ƙwarin gwiwar cewa Odion Ighalo zai haɗa kai da sauran ‘yan wasan da za su buga gasar kofin Afrika ta 2021.

Ƙungiyar Al Shabab ta Ighalo ta ƙi sakinsa a domin fafata gasar.

Wannan ya sa tsohon ɗan wasan Manchester United da Watford ya shiga tsakanin kulob da ƙasar.

An ruwaito Ighalo yana Nijeriya kuma yana da wa’adin tabbatar da kasancewarsa.

“Da fatan Odion ya zo,” inji Eguavoen a wani taron manema labarai a ranar Talatar da ta gabata.

Ana kyautata zaton cewa gogaggen ɗan wasan ne zai jagoranci kai hare-haren na Eagles a yayin da babu ɗan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen.

Odion Ighalo Wanda ya lashe kyautar ɗan wasan da yafi kowanne ɗan wasa yawan zura ƙwallaye a gasar ta AFCON a shekara ta 2019 inda ya zura ƙwallaye 5.

Kuma ya taimakawa Nijeriya wajen lashe gasa inda ta ƙarƙare a mataki na uku na gasar a 2019.