Hana kiwo a Kudu da raba kan Nijeriya

A makon nan ne Ƙungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (NEF) ta mayar wa ƙungiyar gwamnonin kudancin ƙasar nan da martanin cewa, su na gina mutanen da ke da tsananin nuna ƙabilanci da kuma ɓuya a bayan su suna tinzira jamaar su domin raba kan al’ummar ƙasa, wadda sanarwar hakan ke ɗauke da sa hannun Kakakin ƙungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, da suka zargi gwamnonin da suka yi rantsuwar kare kundin tsarin mulki da taimaka wa masu fafutukar raba kan ƙasa da al’umma baki ɗaya.

Ƙungiyar Dattawan Arewan ta bayyana matakin da gwamnonin kudancin ƙasar suka ɗauka na hana yawon kiwo a matsayin wani yunƙurin raba kan ƙasar, wanda irin wannan yunƙurin na gwamnonin kudancin ba shi ne farau ba, domin an sha zargin su da goyon bayan hana mutanen arewacin ƙasar da yin rawar gaban hantsi a shiyyar su, ta fannin kasuwanci, zamantake da makamanta haka.
Wannan martani na ƙungiyar dattawan abu ne da ya kamata a yi nazarin sa sannan a dube shi da idon basira, kana a xora shi a ma’aunin dokoki da kundin tsarin mulkin Nijeriya ta fuskar duban wancan yunƙuri na gwamnonin kudancin ƙasar.

Abu na farko dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ginu kuma tsayu akan bai wa kowane ɗan ƙasa cikakken ‘yancin zama ko rayuwa ko walwala tare da yin kasuwanci a ko’ina kuma a kowane ɓangare na Nijeriya ba tare da tsangwama, kyara da nuna ɓangaranci ko ƙabilanci ba. Kundin tsarin mulkin ƙasa ya yi tanadin dokar da ta kare wa kowane ɗan ƙasa mutuncin sa ba tare muzgunawa ko cin zarafi ba.

Amma sai ga shi ayau an wayi gari ƙarara wasu zaɓaɓɓun wakilan da suka yi rantsuwa akan za su kare kundin tsarin mulki da ci gaba da ɗorewar Nijeriya a matsayin dunƙulalliyar ƙasa sun gaza wajen aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyan su; suka gwammace mayar da hankali wajen raba ƙasa da al’ummar cikin ta.

A kuma lokacin da ake tsaka da fama da matsalar tsaron da ta addabi kowane yanki a faɗin ƙasar nan, maimakon a haɗa ƙarfi da ƙarfe a dunƙule wuri guda don magance matsalolin da ke damun kowa a ƙasar, sai kuma su can suka raja’a wajen bai wa masu fafutukar ɓallewa daga ƙasar da masu aikata laifuffuka da suke tunanin murƙushe hukumomin gwamnatin tarayya da kuma ‘yan arewa da ke yankin domin cimma burin su na siyasa a shekara mai zuwa kamar yadda masu sharhi akan al’amuran yau da kullum ke gani.

Su kuma yankin Kudu maso-Yamma waɗanda zaɓaɓɓun ‘yan siyasar su suka bayar da kai bori ya  hau na taimaka wa masu fafutukar nuna bambancin ƙabilanci domin neman ganin an biya musu buƙatar su ko kuma su bar Nijeriya, yayin da yankin Kudu maso-Kudu ya shiga yanayin tababa da fargaba dangane da wannan yanayi.

Har wa yau, masu sharhi da fashin baƙi akan lamuran yau da kullum suna ganin wannan yunƙuri na hana kiwon sake da gwamnonin kudun suka dunƙule ra’ayin su wuri guda, duk yunƙuri ne na taimaka wa masu fafutikar ganin an raba ƙasa, kamar yadda wasu tsageru a yankin Inyamurai suka soma shekara da shekaru.

Ƙungiyar IPOB mai fafutikar ƙirƙiro da ƙasar Biafra wadda tuni gwamnatin Nijeriya ta haramta, ƙarƙashin shugaban ƙungiyar Nnamdi Kanu, wanda cikin makon nan jaridar Premium Times da ake wallafawa a yanar gizo ta ruwaito cewar Nnamdi Kanu ya yi hayar wani kamfani a ƙasar Amurka mai suna BW Global Group, har sun ƙulla yarjejeniyar shekara guda akan dalar Amurka dubu ɗari 750, kawai don yi masa kamun ƙafa da samun goyon bayan gwamnatin Amurka akan ƙudirin raba Nijeriya gida biyu.

Kamfanin, wanda mallakin Jeffrey Birrel da Alan White ne, kuma aka wa rajista a birnin Washington DC, babban birnin Amurka, ya ƙunshi jamian gwamnatin Amurka, yan majalisar dokoki da sauran masu faɗa a ji na ƙasar, kuma zai duƙufa ne wajen jan hankalin gwamnatin Amurka a game da muhimmancin gwagwarmayar da IPOB take yi da sunan raba ƙasar.

Tambayoyin da suke yawan zuwa wa mutane a rai musamman ‘yan Arewa su ne shin su wa ke ɗaukar nauyin wannan ƙungiya ta IPOB?  A ina suke samun irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe, sannan su waye ke ɗaure musu gindi da ba su goyon baya? Shin jagororin yankin nasu da dattawan su su ma suna goyon bayan da’awar tasu ne? To me ya sa ba sa tsawata masu indai da gaske sun amince da ƙasa ɗaya al’umma ɗaya? Da sauran tambayoyi da yawa makamantan waɗannan.

Ire-iren waɗannan abubuwa ne suka kai ga Ƙungiyar Dattawan Arewa ta kasa yin shiru da bakin ta wajen nusar da gwamnati da kuma mayar wa gwamnonin Kudun da martani don ganin sun bi tafarkin yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba kowane ɗan Nijeriya ‘yancin walwala a ko’ina. Wanda kauce wa hakan kuma zai iya tayar da zaune tsaye a dukkanin sassan ƙasar, ya kasance ana kukan targaɗe sai kuma ga karaya; ba ta mutu ba ta ɓulguce.
Yana da kyau tun da wuri gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin gaggawa akan wannan yunƙuri na gwamnonin kudancin da suke shirin aiwatarwa don cimma wata manufa tasu ta siyasa kamar yadda ake hasashen yankin biyu sun ɗinke ne don fitar da ɗan takarar su guda a zaven 2023 (wanda hakan kuma da kamar wuya, haɗin Yarabawa da Inyamurai).

Ko da yake alamu sun nuna shi kan sa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari abin bai yi masa daɗi ba, tunda ya fito da kakkausar murya ya nuna wa gwamnonin ɓacin ran sa da illar da abin zai iya kawo wa ƙasa. Inda ya ce “Matsayar da gwamnonin kudancin suka cimma a taron da suka yi a ranar 11 ga Mayun nan a Asaba babban birnin jihar Delta, ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki na yanci da walwalar yan ƙasa, na zaunawa da gudanar da kasuwanci a kowane sashe na ƙasar, ba tare da laakari da jihar su ta asali ba”.

Shugaban Ƙasar ya zargi gwamnonin na yankin Kudu da saka siyasa a cikin muhimman alamari na tsaro, yana mai cewa matakin na su ma ba ya kan doka. Ya kuma ce manufar gwamnonin da suka sanya hannu a wannan matsaya ta taron kawai tsagoron siyasa ce da nuna ƙarfin iko.

Sannan ya ce ƙarara yunƙurin gwamnonin ya nuna cewa babu wata maslaha ko mafita da gwamnonin suka samar a cikin matakin da suka ɗauka, wadda za ta warware matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya da ya daɗe yana faruwa a ƙasar.

To me ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi? To akwai buƙatar gwamnati ta himmatu wajen kawo ƙarshen rikici tsakanin manoma da makiyaya da hare-haren taaddanci da ake taallakawa da Fulani makiyaya. Kuma ta shawarci gwamnonin kudancin ƙasar wajen samar da ingantaccen tsarin da zai ba makiyaya damar yin kiwo ba tare da takura wa kowane ɓangare ba, ta hanyar samar da burtalai da killataccen wuri.