Daga AMINA YUSUF ALI
Barkanmu da shigowa wani sabon makon, masu karatu. Kada ku manta da batun da muke tattaunawa da ku a makon da ya gabata wato, kullen da ake yi wa matan aure. Wato yadda wasau mazan kan kulle matansu a gida su hana su fita kuma su hana su mua’amala da kowa. Mun faɗi ma’anar kulle da abubuwan da maza su yi don yin kulle. Mun faɗi guda biyar, hana ta mu’amala sosai da kowa har iyayenta, ƙwace wayarta, hana ta fita, hana ta sana’a, hana ta yin shigar da take so ko da ba ta saɓa wa addini ba. Yanzu za mu cigaba daga na shida. A sha karatu lafiya.
Hanya ta shida kuma ita ce, sanya mata tsoro a zuciyarta da dankwafar da ita. Maza irin waɗannan suna dankwafar da mace ta ma manta wacece ita. Sukan daka wa mace tsawa yadda suke yi wa ‘ya’yansu, wasu ma har da duka. Ko su ƙi kula ta ko hira da ita sai lokacin da suke buqatarta. Duk wai don a sanya mata tsoro a ranta ta ji ita ba komai ba ce ta cigaba da yi musu biyayya ko da a kan savon Allah ne.
Wani har horon yunwa yake mata. Wani kuma har kulle mace yake a gida ya fita da mukullin idan ta ƙi yi masa biyayya.
Sannan na bakwai akwai wani mijin ma saboda tsananinsa dai-dai da abinci sai ya auna mata ya ba ta. Saboda kada ta yi masa almubazzaranci ko ta yi kyauta.
Amma kuma Yayana ka sani, shi yi wa mace kulle tamkar girman kai ba koyarwar addini ba. Kuma tauye haƙƙin ɗan’adam ne. Duk da dai namiji yana ganin mace tana ƙarƙashin kulawarsa ne. Kuma a cikin yi mata tarbiyya ne hana ta cakuɗa da mutane da za su iya canza mata tunani shi ma duk ba laifi ba ne. Amma kada a wuce iyaka.
Sannan rashin yarda ba ƙaramar illa yake kawowa ba a kowacce alaƙa. Mu koma batun waya. Wata matar ba don komai take amfani da waya ba sai don yanar gizo. Kuma yanar gizo nan don sana’a take amfsni da shi. Ta nan take kasuwancinta. Ka toshe mata wannan hanyar ka ƙwace mata waya, kuma kana tsammanin ta so ka ko ta yi maka biyayya tsakani da Allah? Wata fa daga nan ka koya mata munafurci. Kuma da ma takurawa tana kawo haka.
Za ta yi ta boye maka abubuwanta da wasu mutane da take mu’amala da su. Ranar duk da tsautsayi ya sa ka binciko, ka ji zuciyarka kamar za ta buga, saboda tsanannin mamaki. Daga nan ma wataƙila auren sai ya gutsure. Ka rabu da ita, wataƙila ma kuna da yara a tsakani. Ba sai na yi maka dogon bayani a kan matsalar rabuwa da mace mai ‘ya’ya ba.
Haka hana ta mu’amala da nesanta ta da ‘yanuwa ta na jini. Kai kanka ka san ka taro Dala da Gwauron dutse da faɗin kai. Ba za ta taɓa yi maka biyayya ba a kan haka.
Sannan yanke mata alaqa da mutane yana kawo mata tunani da rashin walwala har a kai ga cutar damuwa (depression). Kai ba ka nan, kuma ka ƙi bari ta mu’amalanci kowa. Wataƙila gida ita kaɗai. Kuma idan kana nan ba ka saurarenta. Ko kuma ita tana tsoron hira da kai ta gaya maka damuwarta saboda tana tsoronka. Kuma sam babu yarda a tsakaninka da ita.
Kuma ka sani Yayana, ba fa a yi wa mace dole a biyayya. Ba ‘yarka ba ce. Ka barta ta bi ka saboda Allah, da kuma kyautatawa. Ko ba ka ce ba, idan tana jin daɗin zama da kai za ta bi ka, ko ba ka tursasa ta ba.
Haka ƙuntata mace yana sa watarana ta yi maka bore. Kawai ɗabi’ar mutane ce. Ko yaya ka zafafa wajen ƙuntata mutum har ya kai bango, to watarana dole zai bijire maka. Ko da kuwa ɗanka na cikinka ne.
Haka zai rasa ƙimarsa a idonta don yana nuna mata rashin yarda da son kai, da kuma rashin adalci. Komai za ta yi masa sai dai don tsoron hukuncinsa ba wai don ƙauna da girmamawa ba.
Domin ita yarda tana nuna so. Idan namiji yana kulle mace bai yarda da ita ba. Don haka ba maganar so. Haka idan mace tana sonka, za ta yarda da kai ko da ba ka tursasa ta ba.
Sanban batun sana’a, ka hana mace neman na kanta ta yaya za ta kula da iyayenta da danginta? Ba a ce dole ne barin mace sana’a ba. Amma kyautatawa ce. Kuma ƙaruwar dukkanku ku biyun ce.
Ka sani, idan mace tana sana’a, galibi kuɗin a kan yaranku yake ƙarewa da gidanku. Ɗan abinda take yafa wa iyaye da dangi kaɗan ne. In dai ba wata matsalar ce da ita ba, musamman ta rashin kamun kai ba, to bai kamata ka tauye ta ba. Domin duk abin taimakon juna ne.
Don haka kulle ba ya saya maka so ko biyayyarta. Illa lalata alaƙarku da ta’azzarar da rashin yarda a tsakaninku.
Ina godiya ga masu yi min fatan alkhairi da addu’a har ma da tsokaci da shawarwari. Na gode. Haƙiƙa shawarwarinku suna ƙarfafa min gwiwa. Allah ya kai mu mako mai zuwa.