Na sha tsangwama sanadiyyar tsumburewar jikina, har ya sa ni tunanin kashe kaina – Jarumi Aki

Daga AISHA ASAS 

A cikin wata tattaunawa da Chude Jideonwo, shahararren jarumin barkwanci da ya fito daga Jihar Abiya da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da Aki, ya bayyana yadda tsayawar girman jikinsa ya zama babbar barazana ga walwalarsa tare da samun tsangwar da har ta sa shi tunanin ya kashe kansa ma ya huta.

Jarumin ya bayyana cewa, saura ƙiris ya ɗauki ransa bayan da likita ya tabbatar wa mahaifiyarshi yana tare da laluran tsumburewar jiki, wanda hakan na nufin jikinsa ba zai ci gaba da girma daidai da shekarunsa ba.

Jarumin ya ce, “a matsayina na ƙaramin yaro, kamar kowanne yaro Ina son ababe da dama, sai dai abinda ya faru a lokacin da nake da shekara tara da wata shida da haihuwa ya taka wa ƙurciyata birki.

Har yanzu Ina tuna mutumin, likitan da ya ce da mahaifiyata, madam ɗanki na tare da matsala ta tsumburewar jiki, a wata kalmar  ‘growth reradiation’. A lokacin na fara jin wannan kalmar, kuma ya ɗauke ni tsayin lokaci kafin in iya furta kalmar.

“Tun fa daga nan ƙurciyata ta haɗu da tangarɗa, yara ‘yan’uwana har ma da manya na yawan zolaya ta da rashin girman nawa, tare da hantara da ƙyara, har aka wayi gari na ga ɗaukar raina da kaina a matsayin mafita ga ƙuncin da suke tusamin akan rashin girman jiki.

“Na ma gode Allah da ba a Iko na tashi ba, don wannan tunani nawa da ya fi samun wurin aiwatar da shi sakamakon gadar Third Mainland Bridge da suke da kuma take kusa (Gadar Mainland ta Third Mainland ita ce gava mafi tsayi a cikin gadoji uku da suka haɗa Legas Island zuwa babban kasa).”

Jarumi Ikedieze ya ƙara da bayyana alaƙarsa da ‘yan’uwansa wadda ya bayyana a matsayin marar qarfi, sai dai ya ɗora alhakin haka, kan irin dangantakar da suke yi tsakaninsu da iyayensu, sai dai ya jinjinawa mahaifiyarshi kan irin namijin ƙoƙari da ta yi a rayuwarsa, wadda ya ce, idan ya fara zayyano wannan ɓangare, zuciyarshi zata iya karyewa.

“Idan na tuna irin jajircewa da mahaifiyarmu ta yi wurin kula da mu, da irin faɗi-tashin da ta sha kanmu, zuciyata zata iya karya a take, Ina da matuƙar muradin in dinga kiranta, Ina jin yadda take, sai dai a ɓangarena irin kusanci da alaƙar da mutane suke da ita da iyayensu ne ban samu irinta ba.”

Masu iya magana dai sun ce, abinda ya saka ka kuka wata rana zai iya saka ka dariya, kuma abincin wani gubar wani ce, sannan akwai haske a ƙarshen kowanne kogo.

Da wani zai sanar da wannan jarumin a lokacin da yake cikin ƙuncin cin zarafi da ake yi masa dalilin rashin girman jikinsa cewa, wata rana wannan lalura zata zama sanadin samun shuhura da tarin dukiya gare shi, zai musanta haka.

A yanzu Jarumi Aki na ɗaya daga cikin manyan jarumai da masana’antar Nollywood ke ji da alfahari da su, ba kuwa komai ya zame masa tsani ga wannan nasara ba face laluran da yake da ta tsumburewar jiki, wadda ta ba shi damar fitowa a matsayin qaramin yaro, amma da qwaqwalwar manya, hakan ya sa rawar da yake takawa ta fi wadda za a iya samu a ƙaramin yaro da yake daidai jikinsa. 

Masu kallo sun daxe suna nishaɗantuwa da finafinansa na barkwanci tare da yabawa ƙoƙarinsa wanda a lokacin da yawa suke masa kallon ƙaramin yaro, sai dai soyayyarsu gare shi bata gushe ba a sa’ilin da suka samu tabbacin babba ne mai jikin ‘yan yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *