Abba El-Mustapha ya yi rashin mahaifiya

Daga AISHA ASAS 

Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, kuma tsohon jarumi a masana’artar Kannywood, Malam Abba El-Mustapha, ya yi rashin mahaifiyarshi mai suna Hajiya Aisha wadda ake kira da Gwaggo, a ranar Talatar da ta gabata.

Sanarwar rasuwar wadda ta fito daga ɗan nata Abba El-Mustapha, yayin da ya wallafa a shafinsa na Facebook. 

El-Mustapha ya bayyana rasuwar mahaifiyar tashi cikin jimami, tare da siffanta ta a matsayin rayuwarshi bakiɗaya. 

“Na rasa mahaifiyata kuma duniyata, (Gwagwgo). Ya Allah ka jiƙan ta, ka gafarta mata kurakuranta, ka sa aljanna ce makomar ta. I will mourn you till my last breath Gwagwgo.”

Allah Ya jiƙan Gwaggo Aisha, Ya ba shi haƙurin rashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *