Manyan mutane nawa ke hannun jami’ai?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiya tun mutum na lissafawa har ya tsaya wajen gano yawan manyan mutanen da ke tsare a hannun jami’an tsaro don jiran ko a sake su ko a gurfanar da su a gaban kotu. Hakanan wasu kuma na gidan yari su na jiran yanke hukunci a caji daban-daban da su ke fuskanta.

Abun da na ke nufi da manyan mutane su ne wadanda su ka shahara ko su ka tava riqe manyan muqaman gwamnati. Misali ma kafin na yi nisa a lokacin mulkin shugaba Buhari an yi ahuwa ga biyu daga manyan mutanen da a ka tsare da su ka haɗa da tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye da tsohon gwamnan jihar Taraba Reverend Jolly Nyame.

Kazalika ba za a manta da yadda tsohon mai ba da shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki ya daɗe a tsare ba har ma sai bayan mahaifin sa tsohon Sultan Ibrahim Dasuki ya rasu sannan Allah ya sa ya samu ’yanci ya dawo gida. Can baya ma za mu tuna yadda mai tsaron lafiyar marigayi shugaban mulkin sojan Nijeriya Janar Sani Abacha wato Manjo Hamza Almustapha ya share tsawon shekaru goma sha biyar kafin Allah ya sa a sake shi bayan tsallake hukuncin kisa da ma barazana ga rayuwar sa a gidan yari.

Kowa in ya yi nazari zai iya tuno wani da ya daɗe a gidan yari bisa gaskiya ko akasin haka. Shin kun ma tuna da jigon PDP Bode George wanda bayan yanke ma sa hukuncin ɗauri sai mutane su ka riƙa tururuwa gidan yarin don neman wa imma a sako shi ko kuma ba mamaki su taya shi zaman yarin. Wannan ma fa kan shari’ar almundahana ne.

Hakanan shi ma tsohon gwamnan Delta James Ibori bayan samun kan sa daga ɗauri a London, jama’ar garin su, sun fito sun yi ma sa gagarumar tarba. An daure shi a Burtaniya ne don samun sa da laifin laƙume dukiyar jihar ta Delta to amma ka ga yadda jama’ar jihar sa ke son sa don a nan laifin sa a wajen su bai kai na ɗauri ba sai dai ko kenan a bar shi ya rika yi wa mutane ihsani daga abun da ya samu.

Kafin na fita daga tuna baya, har yanzu fa tsohon ɗan majalisar wakilai Farouk Lawan na zaman gidan yari a Kuje bayan samun ɗaurin shekaru da dama. Ga batun ɗauri Ibrahim Garba Wala in ya karanta wannan rubutu zai yi ajiyar zuciya don bayan an yanke ma sa daurin shekaru da daman gaske ya fara zama a gidan yari a Suleja jihar Neja kafin a cilla shi Argungu a jihar Kebbi inda Allah ya taimake shi a sanadiyyar ahuwar da a ke bayarwa ya shiga cikin jeri a ka sake shi bayan shekara ɗaya.

Duk lokacin da ya gaji da zama a gidan yarin ya kan yi alwashin shiga yajin cin abinci inda ni kuma na kan shawarce shi da sam kar ya fara don ba a irin Nijeriya a ke sauraron masu yajin cin abinci ba. Zai iya shiga yajin har rai ya yi halin sa kuma ba wanda za a zarga don hakan ya zaɓa.

A lokacin da ya fito na zanta da shi inda ya bayyana min shi tamkar makaranta ya shiga don ya gano wani ilimi na daban da bai samu a rayuwar sa ta ’yanci ba sai da ya faɗa gidan yari.

Ba Ibrahim Wala kaɗai ba akasarin waɗanda su ka zauna a gidan yari kan bayyana koyo karatu. Za mu yi ƙoƙarin jin ta bakin tsohon shugaban kwamitin aiki na da cikawa na fansho Abdulrasheed Maina in Allah ya sa mu na raye a lokacin ya samu fitowa daga gidan yari.

Lauyoyi da ‘yan uwan waɗanda su ka daɗe a tsare a hannun jami’an tsaro ko jiran hukunci a gidan yari na nuna damuwa.

Kazalika wani lokacin waxanda a ke tuhuma kan samu beli amma a kan sake kama su don wasu sabbin caji da ke biyo baya.

Misali ga shugaban ‘yan awaren IPOB Nnamdi Kanu wanda ke fuskantar shari’ar cin amanar ƙasa ya samu hukuncin a sake shi bisa yadda a ka cafke shi a Ethiopia a ka dawo da shi gida amma gwamnati ta cigaba da tuhumar sa kan wasu caji inda kusan duk shugabannin siyasar kudu maso gabar ke kira a sake shi da alƙawarin za su sauya ma sa akidar aware.

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai fi ba da labarin yadda dattawan Igbo su ka yi ta yi ma sa matsin lamba ya sake Nnamdi Kanu.

Akwai ma mafi yawan shekarun dattawan Chief Mbazulike Amaechi wanda ya shigo fadar Aaso Rock ya na mai buƙatar kafin ya koma ga Allah shugaba Buhari ya damka ma sa Kanu da alƙawrin zai kula da shi kuma za a daina samun matsalolin rajin ’yan aware. Tsohon shugaba Buhari dai ya a lokacin ya ce zai duba buƙatar amma ba ya katsalandan a lamuran da ke gaban kotu.

Haka shi ma DCP Abba Kyari ya samu beli a ɓangaren shari’ar sa amma a kotu ta biyu a ka cigaba da riqe shi kan tuhumar alaƙa da safarar miyagun ƙwayoyi.

Lauyan sa Barista Hamza Dantani ya ce hatta lokacin da ‘yan Boko Haram su ka fasa gidan yarin Kuje; Kyari ya na zaune a ciki don bin doka don haka ya dace a duba sadaukar da kan sa ga kasa. Dantani ya ƙara da cewa duk tuhumar da a ke yi wa Kyari ba za ta kenan sanya a kauda ido daga irin gudunmawar tsaro da ya ce ya ba wa Nijeriya ba.

A gefen dakataccen shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa wanda ya share fiye da kwana 56 na tsarewa don bincike ba shari’a ya fara zama abun kokawa daga muƙarrabai da ‘yan uwa.

Bawa wanda ya zama shugaban EFCC bayan dakatar da tsohon shugaban ta Ibrahim Magu ya sha samun sukar tamkar an dasa shi ne a wajen don kare muradun wasu masu qarfi a tsohuwar gwamnatin Buhari.

Da ya ke miƙa ƙorafi a zantawa da manema labaru kakakin muqarrabai da magoya bayan Bawa wato ɗan kasuwar canjin kuɗi ta Abuja Alhaji Rabi’u Gada ya ce tun farko gayyatar Bawa a ka yi don amsa tambayoyi amma sai shiru a ke ji har fiye da kwana 56 na iya ƙa’idar tsarewa don bincike bisa umurnin kotu.

Rabi’u Gada ya ce su na ɗaukar riƙe Bawa a matsayin bita da kulli kan ayyukan da ya ce na yaƙi da barayin biro. Gada ya ƙara da zargin cewa yunƙurin Bawa na binciken wasu gwamnoni a ƙarshen mulkin Buhari ya ja ma sa wannan rakai ɗin.

In za a tuna Bawa ya yi takun saka da tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun inda vangarorin biyu su ka caccaki juna kan maqudan kuɗi. Allah ya hukunta a yau Maradun ne ƙaramin ministan tsaro yayin da Bawa ke fuskantar bincike.

A na sa sharhin lauya mai zaman kan sa Barista Modibbo Bakari wanda ya gudanar da bincike kan Bawa, ya dora alhakin ne bisa rashin amsa tambayoyin masu bincike ya jawo jinkirin tafiya kotu.

Bakari ya ce da dai Bawa ya nemi lauyoyi ko ya miƙa ƙorafi gaban kotu da kuwa an wuce wannan hali na dogon tsarewa da ya ke ciki.

Kazalika, Barista Bakari ya ce zai yi wuya lauyoyin kare haƙƙin ɗan adam su fada maganar ba gayyata.

Jagoran muƙarrabai Rabi’u Gada ya ce yanzu za su bi matakan shari’a don kwato haƙƙin Bawa.

Ba kamar a batun kama Godwin Emefiele na CBN da ya ɗauki hankalin lauyoyi da kafafen labarun zamani ba, batun Bawa ya zama sai tashin zance.

Koma a kafafen yanar gizo da ke da sauri da arahar bayyana ra’ayi ba labarun da su ka shafi neman bahasi kan riƙe Bawa. Ta kan yiwu wasu ba su san yadda Bawa ya gudanar ayyukan sa ba ko kuma sunan sa bai shahara kamar na Ibrahim Magu, Ibrahim Lamorde, Farida Waziri ko shugaban hukumar na farko Nuhu Ribadu ba.

Duk da haka mamyan lauyoyi 3 Rotimi Jacobs, Kemi Penheiro da Femi Falana sun buƙaci bin kadun daɗewar Bawa a hannun jami’an tsaro.

Shin ko wane laifi Bawa a matsayin sa na madugun yaƙi da cin hanci ya aikata? Akwai bayanai a yanzu da ke nuna na ba da dama Bawa ya iya ganawa da lauyoyi da ’yan uwan sa.

A nan zan ce am fi jin labarin manyan mutane da su ka kwan biyu a tsare fiye da ɗimbin talakawa da ba a san su ba waɗanda su ka shafe shekaru su na tsare ba tare da ma an kammala shari’ar su ba.

Kammalawa;

Duk mai son adalci a duniya zai yi fatar sashen shari’a ya gyaru wajen aminta daga duk hukuncin zalunci, shaidar zur ko ɗaure ’ya’yan bora a sake na mowa. Duk al’ummar da ta yi nasarar samun kotuna masu inganci da alqalai masu gaskiya da amana, to zai zama da wuya zalunci ya samu gindin zama.

Da zarar an aikata ba daidai ba in an je kotu a ka samu hukuncin adalci to hakan zai zama darasi har ma a fara rasa masu zuwa kotu don danniya za ta zama tarihi.