Har yanzu babu jikan Shata da ya nuna sha’awar ya gaje shi – Yalwan Shata

Spread the love

“Mutuwar aure barkatai na damu na”

Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD 

Hajiya Fatima Yalwan Shata ta na ɗaya daga cikin matan mashahurin mawaƙin Ƙasar Hausa, Marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina. Ta tattauna da Wakilin Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD, inda ta yi ma na bayani game da rayuwarta da ta al’umma, har ma da batun siyasa da kuma zamantakewa, wacce kuma ta taɓo batu dangane da yawar mutuwar aure barkatai a Arewa, ta kuma ba da mafita. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Ko mene ne sunanki na yanka?

YALWAN SHATA: Sunana Hajiya Fatima, amma an fi sani na da suna Hajiya Yalwan Shata, shekaruna 65, Ina da yara uku; Bilkisu, Umma da Jamilu, sannan Ina da jikoki goma sha.

Hajiya, kun ga mulki iri-iri, wacce shawara ki ke da ita ga ‘yan siyasa?

Na taso na fara wayau lokacin da ake siyasar NEPU da NPC a jamhuriya ta farko, sannan aka yi ta NPN da PRP da sauransu a jamhuriya ta biyu, soja suka karvi mulki, aka yi ta musaya har ya zuwa yau. Yankin Kudancin ƙasar nan, ba a kasafai ake sarar wani game da banbancin siyasarsa a wurin kamfe, amma banda a Arewa. Atiku ya kai ziyara a Kaduna aka samu yara suna faɗa da Gariyo. Ita siyasa ai ra’ayi ce, mai dankali ba ya cewa dole a sayi kayansa bayan wasu suna son rogo. Ya kamata ‘yan siyasa su sani, bai dace su ringa ingiza matasa ba, don haka bai dace ba.

Ba wani ɗan siyasa da zai ɗauki nauyin wani ɗan banga da aka kama ba, sai dai a bar wanda aka kama da ya sha wuya shi da iyayensa. Wani kuma ya zo wucewa ma, amma rikicin banga ya rutsa da shi don ya fito talla ko wajen neman abinci amma an sa shi a wahala. Ya kamata a bar banga, muna da jami’an tsaro na hukuma ta ƙasa da su gargadi ‘yan siyasa da su daina sa yara yin banga da miyagun makamai.

Hajiya, mene ne shawarar da za ki bayar ga tarbiyar yara, inda iyaye ke aiki, sun dawo gida a gajiye, an bar tarbiyyar yara ga masu aiki?

Wannan abin na ci min tuwo a ƙwarya. Yaro ya fi jin maganar uban. Ina kira da a samu lokaci a yi musu biyayya. Haƙƙi na uba ne. Idan uwa ta yi faɗa da safe, to uba da ya dawo sai ya ɗora. Uba ya kamata in ya dawo ya tambayi yara ko sun yi Sallah, in ba su yi ba, a tsawata musu. Tabbas yara sun fi jin shakkar uba.

Hajiya, wata ta ƙona yaran kishiyarta a Jihar Neja, wasu sun ce gara mazan nasu su nemi mata masu zaman kansu maimakon a yi musu kishiya! Me za ki ce game da zafin kishi na matan yanzu?

Mu mun tashi a gida ga ɗakin uwa ga na kishiyar uwa. Saboda da kara, sai ka girma za ka gane cewa ai wacce ka ke gunta ba ita ta haife ka ba. Wani gidan, akwai ɗakuna huɗu da falo a tsakiya, wanda ake cewa mu haɗu a falo. Sannan muna da al’adarmu mai kyau wanda ba ma iya kiran sunan kishiya. Sai dai ƙaramar ta ce wa kishiyar ta Yaya babba, watau uwargida ke nan. Amma a yanzu, iyaye suna cewa kar ki yarda, auro ki aka yi, auro kishiyarki aka yi. Bayan kowa ya san Allah fa ya ce maza su auri mata huɗu. Amma yanzu sai ka ji ‘yar Shekaru ashirin ta ɗauki makami ta kashe miji, wata ta sa guba.

A lokacinmu, miji zai ce matarsa ta nemo masa mata ya ƙara aure, watau mace ta nemo wa kanta kishiya. Kuma a zauna sumul kalau. An yin kishi a lokacinmu, amma mai kyau ne, don ana yin gogoriyon ganin an kyautatawa maigida ne. Uwar gida ta ke zuwa ta karɓo masa amarya, kuma a zauna cikin jin daɗi. Shari’a ta yarda Namiji ya auri mata huɗu, amma ba a yarda mace ɗaya ta auri maza biyu ba ko fiye ba. A da ana auren mace huɗu har da ‘kwarkwarori. Ba za a wulakanta ki ba, don me kika ɗauki gaba da sanya guba ga kishiya? In kin yi alkhairi, za a yi wa na bayanki, in kin tafka sharri, za a yi ga naki. Hausawa na cewa, rigakafin sharri kar ka yi. Shi Miji, ai Uba ne, abokin zama ne, kuma wa ko yaya ne.

Ina mafita ga abin dariya da ba da mamaki, inda a yanzu ana yin aure, amma amarya ba ta iya girki ba, sai dai Indomi da shayi da ƙwai?

Mafi yawa, mazan za ka samu suna kuka, idan namaji ya yi magana ba a da lokacinsa, don ana kan waya. Shin waya ce ta fi muhimmanci ko mijin? Ba a sa ido an koyi girki ba. Duk abubuwa ne na taɓarɓarewar rashin tarbiya. Ba a iya kula da mutumci da cikin miji ba. Ya je ya dawo ya sha wahala, an ba shi indomi, kina waya ba ki kawo masa ruwn sha ba, ko wani abu. Ya aure ki ne don ku mutunta juna. Ina kira ga iyaye. Kafin a aurar da yarinya a hana ta yawan yin wayar nan, a sata a kicin a tabbatar ta iya abinici, don komi kyawunki, komi ƙasaitarki, komin giman gidanku, in ba ki iya ba kula da kanki da miji ba, to meye amfanin auren? Sai ka ji bayan wata uku, huɗu aure ya mutu.

Me za ki ce game da waɗanda ake aurowa daga qauye a kawo su Abuja, idan aka yi wa miji sauyin aiki daga Abuja zuwa wani gari, sai mace ta ce ba za ta bar Abuja ta koma ƙauye ba?

Ƙila matar ba ta son mijin ne. A lokacinmu, idan miji yana kogon dutse ya ce ki je, za ki je kogon dutsen. Saboda Allah kika sa a gaba. Abuja kawo kuwa kawo ki aka yi, ba garinku ba ne. Kila ma inda aka ma ida shi ya fi ni’ima. Idan misali aka mayar da miji, Funtua, sai mace tace ba za ta je Funtua ba, wannan ba dalili ba ne. indai kina da biyayya, Abuja akwai tsadar rayuwa, idan ya ce ya mai da ke gida zai rinƙa zuwa ƙarshen mako, amma sai ki tayar wa kanki da hankali, bai kamata ba.

Shin ko akwai jikan da yake so ya gaji Mamman Shata a kiɗa da waka?

Ba a samu ba tukun, sai dai gaba. Idan an bunƙasa, ana samun ɗan gado, jikoki ba su fara ba.

Wane kira ki ke da shi game da faɗa tsakanin Hausawa da Fulani?

Wanda ya ba shekaru 60, ya san ba a faɗa tsakanin Hausawa da Fulani kuma ya dace Gwamnati ta  yi maganin abin. Manomi da makiyayi. Hada ake har ana cewa Hausa-Fulani. An yi sakaci har abin ya buwayi kowa. Gwamnati ta dage don dawo da zaman lafiya tsakanin Manoma da Makiyaya. Sai an yi noma da kiwo sannan za a sami abinci da nono da madara. An shiga damuwa da wahala matuka. Lokaci ya yi don Gwamnati ta dage don a sami zamna lafiya.

Wacce jam’iyya ki ke yi?

Ni uwa ce mai son ganin an tallafa wa jama’a a ko da kowace jam’iyya ce ke mulki, ni uwa ce ga kowa, watau kowa nawa ne.

Muna godiya bisa lokacinki da kika ba mu.

To, ni ma na gode sosai.

By Editor