Harin jirgin ƙasa: Har yanzu ni masoyin Buhari ne, inji fasinjan da ya kuɓuta

Daga SANI AHMAD GIWA

Ɗaya daga cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, Barista Hassan Usman, ya ce har yanzu shi masoyin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne.

A ranar 28 ga watan Maris, wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jirgin ƙasa da ke kan hanyar Kaduna, inda aka kashe mutane da dama, aka kuma yi awon gaba da wasu.

Hassan na daga cikin fasinjoji huɗu da aka sako daga hannun masu garkuwar a ranar 25 ga watan Yuli.

Da yake magana a wata hira da ICIR, ya ce duk da cewa gwamnati mai ci ta gaza a fannin tsaro, amma har yanzu; “Ni ina matuƙar son Buhari.

“Har yanzu ni masoyin Buhari ne, amma ta fuskar tsaro zan iya bai wa wannan gwamnati maki kaɗan, domin ɗaya daga cikin babban nauyin da ke wuyansu shi ne ganin gwamnati ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa,” inji shi.

“Amma kamar yadda yake a yanzu, zan iya cewa gwamnati ta gaza sosai a fannin tsaro. Duk da ɗimbin kuɗaɗe da aka ware domin tsaro a Nijeriya, babu wani abu da ake gani a ƙasa.”

Ya ƙara da cewa abin da ya fuskanta a lokacin da yake tsare yana da matuƙar muni.

Idan za a iya tunawa, a ranar Lahadi 24 ga watan Yuli, 2022, a wani faifan bidiyo wanda ‘yan bindigar suka watsa wanda suke dukan waɗanda suka yi garkuwa da su, kuma suka yi barazanar yin garkuwa da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai.